Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya amince cewa iyakokin Nijeriya na ci gaba da fuskantar barazana daga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ta’addanci – ciki har da sabbin kafuwa irin su Lakurawa da Mahmudawa.
Amma, ministan ya tabbatar wa ‘yan aasar cewa gwamnati na ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron waɗannan iyakokin da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa.
Da yake jawabi a taron manema labarai na Minista na 2025, Abubakar ya bayyana irin ƙalubalen da ake fuskanta yayin da ya jaddada ci gaban da aka samu wajen daƙile kutse a kan iyakokin ƙasar.
Da yake mayar da martani kan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankuna irin su Katsina da Zamfara, Ministan ya yi nuni da cewa an samu ci gaba sosai, kamar yadda aka buɗe muhimman hanyoyi da kasuwanni a yankunan Jibia da Basari.
Duk da waɗannan ci gaban, ya yarda cewa wasu ƙananan hukumomi na ci gaba da fuskantar barazana, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ɗaukar matakin soji don ƙwatowa da kuma samar da tsaro a yankunan.
Abubakar ya kuma amince da ƙaruwar ƙalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta musamman a yaƙi da ta’addanci.
Musamman ma, ya bayyana ɓullar sabbin ƙungiyoyin ta’addanci irin su Lakurawa da Mahmudawa, inda ya ƙara da cewa ƙungiyoyin da aka sani da suka riga sun yi aiki a kan iyakokin Nijeriya.
Ya jaddada cewa dole ne jami’an tsaron ƙasar su tashi daga maida hankali zuwa matakin da ya dace wajen magance waɗannan barazanar.
Ma’aikatar tsaron ta ƙara bayyana nasarorin dabarun da ƙasar ta samu a baya-bayan nan da kuma ƙalubalan da take fuskanta a wani yanayi na tsaro na duniya da na yanki da ke ƙara taɓarɓarewa.
Ministan ya jaddada ƙudirin Nijeriya na kare al’ummarta tare da jawo hankali kan illar ta’addanci, da illar rashin zaman lafiya a yankin Sahel, da kuma buƙatar ƙarfafa hadin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa.
“A matsayinta na ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka, zaman lafiyar Nijeriya yana da nasaba da na nahiyar da kuma tsarin tsaro na duniya baki ɗaya.
