Yadda ɗan shekara 18 ya ɗirka wa ‘yan mata 10 ciki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani matashi ɗan shekara 18 da aka tura koyon sana’a ya yi wa ‘yan mata 10 ciki a cikin watanni biyar kacal, ciki har da ‘yar ubangidansa da kuma ’yar talle a Jihar Anambra.

Kwamishinar mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra, Ify Obinabo wadda ta bayyana hakan ta ce an tura shi ne da farko domin koyon sana’a a ƙarƙashin wani mutum, amma a cikin watanni uku ya ɗirka wa ’yar ubangidan nasa da wata ‘yar talla ciki.

Hakan ya sa aka kore shi daga wajen sana’ar.

Daga nan ya koma ƙauyensu, inda ya yi wa wasu mata takwas ciki.

Obinabo ta yi kira ga jama’a da su ba da shawara kan yadda za a magance matsalar, tana mai tambayar ko halin yaron wani abu ne na asiri.

Ta ce, “Ina son shawara daga jama’a domin wannan ya fi ƙarfina.

“Wannan yaro an tura shi koyon sana’a yana ɗan shekara 18, amma watanni uku yana koyan sana’ar ya yi wa ‘yar ubangidansa ciki da ’yar talla.

An bayyana cewa mahaifiyar yaron ta nemi taimako daga Obinabo, inda ta nuna damuwa da halin da ake ciki.

A cewarta, mahaifiyar ta ce, “‘Duk lokacin da na ga yarinya ta zo gidanmu a zamanin yau, zuciyata ɗar-ɗar take yi, don Allah, ina buƙatar taimako.”

Yaron ya shaida wa Obinabo cewa yana shawo kan ‘yan matan ne ta hanyar shaida musu cewa yana son su kuma yana shirin auren su da zarar ya samu dukiya.

By ukarofi