Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Hon. Alhajiji Nagoda mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkar yaɗa labarai kuma wanda ya wakilci Hon. Abdullahi Ibrahim Wayya, Kwamishinan yaɗa labarai na Kano ya bayyana cewa shi da abokin aikinsa Hon. Zawa’i da suka kawo wa gwamna labarin halin da tsofaffin kansiloli tun daga na 2014 zuwa 2024 suke ciki, gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kuma suka ba shi shawara kan ya biya su kuma ya yarda ya biya su su kimmanin 3000 ba tare da la’akari da yadda wasu suka nuna masa hamayya da adawa kasancewa ba jam’iyyarsu ɗaya ba kuma aka fara biyan 903 a wannan Larabar, inda kuma za a cigaba kamar yadda aka tsara aka kasasu uku to abinda gwamnan Kano da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo suka yi wannan ni dai na fi tsofaffin kansilolin murna kan wannan labari da shawara da muka bawa gwamnan Kano ya yi aiki da ita muna godiya Ubangiji muna gode wa gwamnan Kano da ɗaukacin jami’an gwamnatin Kwankwasiyya bakiɗaya da jagoranta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Shi ma jagoran gwagwarmayar nema wa tsofaffin kansiloli haƙƙinsu wanda haƙarsa ta cimma ruwa a ranar Laraba Hon. Sunusi Kata Madobi, ya ce ya yaba wa gwamnan Kano kan wannan alƙawari da ya cika kuma wannan tasa ya bar tafiyar jam’iyarsa ta APC ya koma Kwankwasiyya har abada domin gwamnatinsu ta baya sun biya kansu amma ba su biya tsofaffin kansiloli ba duk da bautawa jam’iyyar APC da suka yi.
Shi ma Hon. Mustapha Muhammad ƙiru ya bayyana wannan rana a matsayin rana da suka samu ‘yanci kai na yin sana’o’i da biyan basusuka da kuma ɗora ɗamara na tabbatar da gwamnati mai tausayi irin ta gwamna Abba na Kano a 2027 da ikon Allah a cewar Hon. Kiru.
Shi ma Hon. Hudu Abdu Takai shugaban ƙungiyar kansiloli masu gafaka, ya ce yana ɗaya daga cikin ɗaruruwan tsofaffin kansiloli da suka ga alat ɗin kuɗi a ranar Laraba, inda ya ce “wannan ba ƙaramin alkairi ba ne kuma ga shi nan da ‘yan kwanaki za a kammala aikin kilomita 5 a ƙaramar hukumar Takai wanda tsohon gwamnan Kano jagoran Kwankwasiyya ya fara aikin a wajen 2013 tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ƙi ƙarasawa, to ga Kalifan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Alhaji Abba Kabir Yusuf cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.”
Tun da farko a jawabinsa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya bayyana cewa waɗannan kansiloli da ba a biya ba tun daga 2014 zuwa 2024 an ware kuɗi ne wajen biliyan 16 da za a biya su daki-daki na farko ‘yan 2014 zuwa 2018 su 903 su aka fara a ranar Laraba, sai kuma kaso na biyu da za a biyasu wata biyu masu zuwa a watan Mayu da Yuli adadin su ne 1188 sai kuma na 2018 zuwa 2024 sai kuma 2021 zuwa 2024 adadin 1371 wanda kuma a ƙarshe gwamnan ya yi alwashin biyansu lokaci ɗaya in damar hakan ta yiwu maimakon Nuwamba da Disamba na 2025 da aka tsara yin hakan.
