Sharif da Dogon Nama za su kawo wa kasuwar Kwari cigaba – Nakabaz

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Alhaji Auwalu Nakabaz wanda aka fi sani da Top Nice ya bayyana cewa naɗa Alhaji Abdullahi Sharif Namalan shugaban riƙo na kasuwar Kantin Kwari zai kawo wa kasuwar cigaba domin a ɓangaren ƙungiya nemo shi aka yi aka ba shi riƙon shugaban ƙungiyar kasuwar saboda ya cancanta kuma zai yi ƙoƙari mai yawa wajen haɗa kan ‘yan kasuwa da bunƙasa kasuwanci a wannan lokaci, don haka suka nuna goyon baya da addu’a ga dukkan wani abu da zai kawo wa kasuwar Kanti Kwari da Kano baki ɗaya cigaba.

“Haka kuma mun san cewa MD Sa’adu Hamisu Dogon Nama ɗan kasuwa ne mai kishin kasuwanci, kan haka ne aka ba shi shugaban na kasuwar Kantin Kwari wanda shi ne babban wakilin kuma ido na gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kuma kowa ya san Gwamnan Kano mutum ne mai kishin kasuwanci da al’ummar Kano baki ɗaya.”

A ƙarshe Alhaji Auwalu Nakabaz Top Nice ya yi ƙira ga ‘yan kasuwa manya su haɗa kansu domin in suna haɗa kansu suma ƙananan ‘yan kasuwa haka za su kasance yadda zai zama an taimakawa marasa ƙarfi su samu cigaba domin a tallafawa al’umma gaba ɗaya kuma abinda Maragayi Alhaji Ahmad Ubale Rahimahullah ya yi musu tarbiyya shi ne a haɗa kai a tausayawa na ƙasa a taimaki al’umma, don haka kullum nasiharsa kenan kuma nasihar da za su cigaba da yi wa al’umma kenan. Ya kuma yi addu’ar zaman lafiyar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi