Gwamnonin PDP sun zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da dabarun tsoratarwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da dabarun tsoratarwa tare da maida su saniyar ware.

Gwamnonin na PDP sun sha alwashin ain yarda da irin waɗannan matakai tare da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da mulki na gari.

Sun bayyana hakan ne yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) karo na 99 na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya bayyana irin ƙalubalen da jam’iyyar da mambobinta ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin da ke mulki ta haifar da yanayi na musamman da ke cike da matsaloli, tunzurawa da kuma canje-canjen yanayin siyasa.

Ya ce, PDP na fuskantar ƙalubalen sauya sheƙa daga wasu mambobinta da kuma tattaunawar kafa ƙawance da wasu, wanda hakan ya shafi wasu ’yan jam’iyyar.

Sai dai ya jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai da jajircewa ga manufarta.

“Duk da waɗannan matsaloli da muke fuskanta, mambobinmu sun ci gaba da kasancewa masu kishin jam’iyya da jajircewa.”

“Babu irin nau’in tsoratarwa ko ƙoƙarin jan hankali da mu a matsayinmu na zaɓaɓɓun gwamnoni, ba mu fuskanta ba. Amma duk da haka, mun tsaya tsayin daka,” inji Gwamna Bala Mohammed.

Bala ya ƙara da cewa, haɗin kan da ke tsakanin ’ya’yan PDP shi ne abin da ke bambanta su da sauran jam’iyyu da ya bayyana da cewa sun tarwatse, inda suke da rassa daban-daban masu rikici.

Gwamna Bala ya ce, “Sauran jam’iyyu sun rabu gida biyu, suna da ɓangarori daban-daban da ke rikici tsakaninsu. Amma babu shakka, PDP na nan daram, muna tafiya tare da haɗin kai.”

By ukarofi