INEC ta tabbatar da aminin Wike a matsayin sakataren PDP

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Zartarwa na Jami’iyyar PDP na ƙasa ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas, ya sanar da taron kwamin karo na 99 a ranar Talata cewa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta amince da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren Jam’iyyar na ƙasa.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta kafa wani kwamiti mai mutane uku ƙarƙashin jagorancin Kefas, tare da Gwamna Dauda Lawal (Zamfara) da Peter Mbah (Enugu), mai ba PDP shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade SAN, a matsayin mambobi, domin tabbatar da ko INEC ta amince da Anyanwu, mai biyayya ga Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin sakataren jam’iyyar.

Wasu majiyoyi da dama ciki har da wani mamban hukumar zaɓe da suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa kwamitin na Kefas ya sanar da taron kwamitin na 99 a ranar Talata a Abuja cewa INEC ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa bisa ga hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke.

Domin tsige shi yadda ya kamata bisa ga shawarar da gwamnonin PDP suka ɗauka, kuma bisa bin sanarwar kwanaki 21, jam’iyyar na shirin sake zama a ranar 30 ga watan Yuni.

Wannan ci gaban dai na iya ƙara dagula rikicin da ke faruwa a jam’iyyar da kuma ƙara ruruta wutar ɓaraka tsakanin jam’iyyar da ministan babban birnin tarayya, wanda ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar da aka ƙulla da shugabannin jam’iyyar a baya don magance rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.

By ukarofi