Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu murnar cikar shekara biyu a kan karagar mulkin ƙasar.
A cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, da kuma ke ɗauke da sa hannunsa, Muhammadu Buhari ya roƙi al’umma da su ci gaba da ba gwamnatin jam’iyyar APC cikakken goyon baya.
Ya ce a daidai lokacin da jam’iyyarsu da kuma gwamnatin ke wannan bikin, ya dace ‘yan Nijeriya su san da cewa tsarin shugabanci abu ne da ke ci gaba da gudana.
Ya kuma ce sannu a hankali za a cimma nasara a sabbin tsare-tsaren gwamnati mai ci, idan an saka haƙuri domin ba abu ne da za cimma a dare ɗaya ba.
Kazalika, Buhari ya ce bai kamata a siyasantar da wasu manufofin da ɗaukar su ya zama wajibi ba.
Ya ce yana goyo bayan ƙoƙarin da gwamnatin APC ke yi na rage talauci da tashin farashi, da ya ce sun yi matuƙar shafar rayuwar talakawa.
Tsohon shugaban Nijeriyan ya ƙara da cewa matakan da ake ɗauka na rage talauci da tsadar rayuwa, ba abubuwa ne da ya kamata a bar gwamnati ita kaɗai da yin su ba.
Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasar da kada su karaya a kan makomar Nijeriya
“ɓangarori masu zaman kansu da dukan mu ‘yan Nijeriya ya zama wajibi mu haɗa hannu domin bayar da gudummuwarmu,” inji tsohon shugaban Nijeriyar, Muhammadu Buhari.
