Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan ayyuka Dave Umahi ya ce dukkan gwamnonin yankin Kudu maso gabas suna goyon bayan shugaba Tinubu inda ya buƙaci waɗanda ba su yanke shawara ba kamar Peter Obi da su bi sahun sauran gwamnonin.
Sannan ya ce an kusa kammala aikin titin Lahadi zuwa Calabar kuma daga watan Disamba masu amfani da hanyar za su riƙa biyan haraji.
Mista Umahi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a yayin shirye-shiryen murnar cika shekaru biyu da hawan mulkin shugaba Tinubu.
Ya ce dukkan gwamnonin yankin Kudu maso gabas suna goyon bayan gwamnatin Tinubu ko da kuwa a wata jam’iyyar suke.
A cewar ministan, yankin Kudu maso gabas na samun ayyukan raya ƙasa daga gwamnatin tarayya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
“Igbo mutum ne ɗan kasuwa da Allah ya bai wa hikima. Abin da Ndi Igbo suke so shi ne adalci – Nijeriya mai cike da daidaito. Kuma abin da shugaban ƙasa Tinubu ke yi kenan.”
“A baya, a lokacin da nake gwamna da mataimakin gwamna, babban abin da ke damun mu a Ebonyi shi ne rashin samun ayyukan gwamnatin tarayya. Amma a yau, ba wanda yake iya tuna wannan. A ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, akwai ayyuka kusan 4 da gwamnatin tarayya ke yi a jihar Ebonyi.”
Ya ce, duk da ‘yan yankin na kukan an mai da su saniyar ware, amma shugaba Tinubu na ƙoƙarin magance wannan matsala musamman na rashin ayyukan more rayuwa da rabon muƙamai.
“A yau, yankin Kudu maso gabas na da ministan ayyuka a karon farko kuma ga ayyuka a ƙasa – titin Fatakwal zuwa Enugu zuwa Abakaliki da titin Enugu-Onitsha da titin Onitsha-Owerri, da gadar Neja ta biyu. Kuma tuni shugaban ƙasa ya biya kaso 30 na kuɗin aikin.
“Dukkan gwamnonin yankin ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke ba, za su mara wa shugaban ƙasa baya. Muna ma tunanin hada wani gangami tare da kuma shugabannin yankin Kudu maso gabas domin mara wa shugaban ƙasa baya a zaɓen 2027.
Muna so a ƙarasa mana ayyukan da aka fara kuma a ƙarfafa haɗin kan da ake da shi da shigo da yan kabilar Igbo cikin al’amurran gwamnati.”
Mista Umahi ya buƙaci dukkan shugabannin adawa a yankin da su haɗa kai da shugaban ƙasa domin cigaban yankin.
“Shugabanci ba abu ne na kai kadai ba. Abu ne da ya shafi al’umma. Idan wani ya riga ya fara bin da kake fatan ka yi ga al’ummarka, sai ka mara masa baya. Ina kira ga ‘yan uwana da shi kansa mai girma Peter Obi da su shigo domin yin aiki da shugaba Tinubu.”
Ya kuma bayyana cewa muhimman ayyuka da suka haɗa da titin Lagos-Calabar da titin Sokoto-Badagry da titin da ake dab da amincewa da shi na Ogun-Ondo-Niger Corridor— ayyuka ne da suke kamar zuba jari ne domin bunkasa tattalin arziki da haɗin kan ɓangarorin Nijeriya.
Sannan game da titin Lagos-Calabar, ministan ya ce an yi kaso 80 na aikin titin kilomita 47.47 daga Ahmadu Bello zuwa tekun Lekki da mahaɗar Eleko. Sannan ana cigaba da aikin ɓangare na biyu na titin kilomita 55 daga Eleko zuwa iyakar Lagos-Ogun.
“Kwanakin baya ne muka ƙaddamar da aikin sashe na 3 ma titi mai tsayin kilomita 65 a Kuros Ribas da kilomita 27 a Akwa Ibom. Kuma irin murnar da mazauna yankin ke yi ya nuna irin jin daɗi da suka yi na ayyukan.”
Sannan ya ce titin Sokoto-Badagry aiki ne da zai kafa tarihi saboda irin muhimmancinsa kuma aiki ne da aka tsara tun lokacin mulkin Shehu Shagari.
“Wannan titi na kasuwanci ya samo asali ne tun lokacin Turawan mulkin mallaka. Shugaba Tinubu yana ta aiwatar da waɗannan ayyuka.”
Daga nan ne ya yaba wa jagorancin shugaba Tinubu yana mai cewa, “Allah ya ba shi hangen nesan son yin aikin Lagos-Calabar shekaru bakwai da suka wuce. A yau, yana tabbatar da wadannan ayyuka wanda ke nuna irin yadda ya himmatu wajen ayyukan raya ƙasa da kyakkyawan fata ga ‘yan Nijeriya.”
Daga nan ya jaddada cewa ayyukan na da muhimmancin da tarihi ba zai manta da su saboda tasirinsu na tattalin arziƙi da samar da cigaba.
