Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, a matsayin annoba da ya kamata a kore shi daga jam’iyyar PDP.
Lamido ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi da shi a Abuja a jiya Talata.
Ya bayyana cewa ko da yake har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, wacce ya taimaka wajen kafuwa ya yanke shawarar dakatar da halartar tarukan shugabanci na jam’iyyar – duk da zafin hakan – matuƙar Wike da tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, na ci gaba da zama mambobin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar.
Tsohon gwamnan ya yi mamakin yadda ake kokarin tilasta wa jam’iyyar karɓar Sanata Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren jam’iyyar na ƙasa, duk da cewa yankinsa, gwamnoni da Kwamitin Amintattu (BOT) sun ƙi amincewa da shi.
A lokacin da aka tambaye shi game da rawar da Wike ya taka wajen rufe ofishin PDP na ƙasa, Lamido ya ce: “To, me mutum zai ce? Wannan ai wani wasan kwaikwayo ne na siyasar Nijeriya.
“Ga mutum wanda PDP ta girmama, ta ba shi matsayi, yanzu kuma ya dawo yana yaƙar jam’iyyar da ta kawo shi. A gaskiya, Wike annoba ne. Abin da yake yi ba dabi’ar Afirka ba ce, balle ta Nijeriya.
