Jam’iyyar ADC a Kano ta yi taron gangami da jam’iyyu don ƙwace mulki a hannun APC

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jam’iyyar ADC mai alamar musabaha reshen jihar Kano, ta gudanar da taron gangamin na ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyu domin yanda za a haɗu domin a tunkari kawar da jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa.

Taron ya sami halartar dukkanin musu ruwa da tsakin jam’iyyar ADC na jihar da wakilan wasu jam’iyu da suka haɗa da PDP da PRP da sauran wasu jam’iyyun da kuma wasu  malaman jamia da suka gabatar da jawabai akan abinda ya shafi haɗin kai.

A yayin taron daya gudana a ɗakin taro na Mumbayya  tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023.Malam Ibrahim Khalil a jawabinsa ya bayyana jam’iyyar ADC itace tamkar jirgin Annabi Nuhu ga ƙasar nan don ta sha banban da dukkan sauran jam’iyyu domin akwai adalci da kuma girmama  ɗan adam a cikinta da baiwa kowane mutum haƙƙinsa.

Ya ce a jam’iyyar ADC. iyaye  Mata da mutane masu buƙata  ta musamman ba zasu sayi fom ba, kyauta za a basu a dukkan takara da zasu nema su  tsaya sannan suma matasa da basu kai shekaru 40 ba suma kyauta za a basu fom   wannan kaɗai sun bambanta ADC da duk wata jam’iyya da take a ƙasar nan.

Sheikh Ibrahim Khalil yace jam’iyyar ADC itace wacce zata karɓi kowa da  irin halinsa sannan kowa zai sami abinda ya dace dashi ba tare da an zalunce shi ba, kuma shi ba zai sami damar  ha’inci ba kuma wanda za a tunkara  yanzu sai an tashi anyi yaƙi sosai a kanta domin ita jam’iyyar APC kamar balam- balam ce wacce idan kana hurawa in ta cika sai ta fashe haka zata fashe  ko  akan rikicin  takara  ko idan an kayar dasu su yi rigama.

Shi ma wanda ya yi takarar mataimakin Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADC.Dakta Aminu Anas Abdurrahman   ya ce sun godewa Allah da ya basu damar gudanar da taron cikin nasara kowa yasan an shaƙe  ƙasar nan.Muhimmin abu shine kula da zaman lafiyar al’umma da dukiyar su da kare rayuwarsu.

Ya ce ƙasar nan gaba ɗaya ana ganin irin abinda yake faruwa ana shugabanci da babu alƙibla, babu damuwa da  menene ke faruwa ga mutanen ƙasa, ba yanda za a yi kana shugabancin mutane, abinda ya dami mutane ba shine ya dame ka ba, duk fariyar wannan Gwamnati na cewa ana tara kuɗi ne wanda ba shine tsarin  tattalin  arziƙi ba, 

Tsarin tattalin arziƙi shine ka  sauko kayi tunanin menene  zai zama rufin asirin al’ummar ka, mutane kada  su riƙa zama cikin fargaba da zulumi wanda ake ciki yanzu a  kusan dukkan ƙasar nan musamman ma a  Arewa da ake a cikin fargabar tsaro.

Dakta Aminu Anas Abdurrahman yace wannan haɗaka  da za a yi a jam’iyyar su ta ADC  anyi  kira sun amsa kuma suna roƙon Allah ya dafa musu, wanda duk suka zo suka ce sun yarda da  tafiyar  Allah yasa da yaƙinin gaskiya suke .

Shi ma shugaban jam’iyyar na ADC na jihar Kano.Hon Musa Ungogo yace taron na ganganko ne da ake so a haɗu don ceto  yan ƙasa da suka shiga mawuyacin hali sanadiyyar Gwamnatin APC  wanda sai lallai an haɗa kai  an kawar da wannan Gwamnati da suke abinda suka ga dama  domin  dama shugaban ƙasa yace kujerar saya  ya yi har yau, ta kai ma so yake idan ya tsufa sosai ko ya mutu yasa ɗansa tunda ɗansa na zagaye yana rabon dafaffiyar taliya..

Ungogo ya ce ya zama wajibi su taimaki al’ummar ƙasar nan domin duk a jam’iyyun ƙasar nan ADC ce bata da rigima ,bata da wata Shari’a a kotu,tsarkakakkiyar jam’iiya ce  ba kamar sauran jam’iyyu ba da ake ta raba kansu,dan haka duk masu kishi za su baro jam’iyyarsu su dawo ayi gangami na runduna masu gaskiya da amana a ADC  a karɗi ƙasar nan a ceci al’ummarta.

By ukarofi