2027: Hamza Al-Mustapha zai nemi takarar Shugaban ƙasa a SDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon babban hafsan tsaron Marigayi Janar Sani Abacha, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.

Al-Mustapha ya ce zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Social Democratic Party.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Minna, babban birnin jihar Neja yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyar na jihar da magoya bayansa.

Da yake jawabi a wajen taron, Al-Mustapha ya bayyana cewa a shirye yake ya jagoranci Nijeriya da gaskiya da kuma tsantsar tsari na gyara ƙasar.

“Na ji zafi kuma na damu matuƙa game da halin da al’ummar ƙasar ke ciki a yanzu, duk da haka, da kyakkyawar alƙibla da jajircewa, Nijeriya za ta iya sake tasowa.

“Ko da yake hanyar da ke gaba na iya zama mai tsauri, tare za mu iya sake gina Nijeriyar da muka cancanta,” inji shi.

Ya bayyana cewa ziyarar tasa wani ɓangare ne na shirin ganawa da masu ruwa da tsaki a faɗin Nijeriya domin tunkarar zaɓen 2027.

Daraktan yaɗa labarai na yaƙin neman zaɓensa, Jubril Umar Sanda, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Al-Mustapha ya “shirya tsaf don tafiyar da ke gaba, a shirye yake ya yi hidima cikin gaskiya, jajircewa, da cikakken shiri na ci gaba.”

Tun da farko, Al-Mustapha ya tsaya a Minna a hanyarsa ta zuwa Mokwa domin jajanta wa waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa wanda ya shafi sama da mutane 200.

Ya jaddada buƙatar samar da ingantaccen jagoranci da haɗin kai don magance ɗimbin matsalolin Nijeriya.

Shugaban jam’iyyar SDP a jihar Neja, Buhari Yarima, ya yi maraba da matakin Al-Mustapha, inda ya yaba da sadaukarwar da ya yi wajen yi wa ƙasa hidima.

“Muna da yaƙinin cewa tare da sahihan ‘yan takara da kuma kyakkyawan hangen nesa, SDP za ta kasance mai ƙarfi a 2027,” inji Yarima.

By ukarofi