Zaɓen Gwamnan Kogi: INEC ta bayyana lokacin da za ta sake zaɓe a wasu mazaɓu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ya zuwa ranar Asabar mai zuwa za ta sake zaɓe a wasu mazaɓu da aka dakatar da zaɓensu yayin zaɓen gwamna a Jihar Kogi.

Ta ce za a sake zaɓen ne a unguwanni guda tara da ke mazaɓar sanata ta tsakiya a jihar.

Wuraren da aka dakatar da zaɓen suna yankin Ƙaramar Hukumar Ogori/Magongo ne a jihar.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ya bayyana a ranar Lahadi cewa, za a sake gudanar da zaɓen a mazaɓun da lamarin ya shafa ne a ranar 18 ga Nuwamba daidai da Sashe na 24(3) na Dokar Zaɓe ta 2022.

Babban ofishin INEC ya ce ya samu rahoton cewa an samu wasu takardun sakamakon zaɓe da aka cike tun kafin ma a kaɗa ƙuri’a.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne a unguwanni tara daga cikin goman da ake da su a yankin Ƙaramar Hukumar Ogori/Magongo.