Da Ɗumi-ɗumi: INEC ta ayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Imo

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar, Hope Uzodimma, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da ya gudana a jihar a ranar Asabar da ta gabata.

A cewar baturen zaɓen da ya jagoranci tattara sakamakon zaɓen, Abayomi Fasina, Uzodimma ya lashe zaɓen ne da ƙuri’ 540,308.

Yayin da ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, ya rufa masa baya da ƙuri’u 71,503.

Ɗan takarar Jam’iyyar LP, Sanata Athan Achonu ne ya zo na uku a zaɓen inda ya tsira da ƙuri’u 64, 081.