Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Jihar Kebbi qƙarƙashin jagoranacin Alhaji Faruk Musa Yaro ta bai wa maniyyata wa’adin sati biyu da su kammala biyan kuɗin kujera.
Ya yi wannan bayanin ne a yayin wata ganawa ya yi da shuwagabannin ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya da ke jihar.
Alhaji Faruk Musa ya bayyana wa shuwagabannin ƙananan hukumomin irin ƙoƙarin da hukumar ke yi na ganin an samu ingantaccen aikin Hajji da za a gudanar a shekarar 2024 mai zuwa.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa ya zama wajibi ga dukkan maniyyaci ya gaggauta biyan kuɗin kujerarsa kafin nan da sati biyu saboda wanda shi ne zai tabbatar da cewa ya ɗauki ƙudurin aikin Hajji saboda yanzu hukumar Alhazai ta ƙasar Saudiyya ita ce ta zo da sababbin tsare-tsaren yadda kowane maniyyaci zai samu VISA kafin wata uku da tashi zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya kuma ja hankalin shugabannin ƙananan hukumomin da su ja kunnen Alhazai daga ƙananan hukumominsu da su bai wa maraɗa kunya su kasance jakadu nagari a ƙasa mai tsarki saboda duk wanda aka samu da laifi babu makawa za a ɗauki matakin ladabtarwa kansa.
Hakazalika ya bayar da tabbacin hukumar jin daɗin Alhazai a shirye take don ganin an bai wa kowa haƙƙinsa.
