Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ta bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka qara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin “karan-tsaye” ga dimokraɗiyya.
Jam’iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Nijeriya ne da “amfani da qarfin iko” wajen tanqwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta.
“Shari’ar Nijeriya ta zama kamar rawar ‘yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya,” inji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi.
Ya ce dalilan da mutanen nan ke gabatarwa suna kwace zaɓen nan, akasari batutuwan da suka shafi kafin zaɓe ne. A cewarsa, Kotun Ƙoli ta yanke hukunci da cewa: “Ba abubuwa ba ne da suka shafe ta, a hukuncin da ta bayar kan ɗan takararmu, Atiku Abubakar”.
Ya yi iqirarin cewa batun shari’ar, wata matsala da ka iya shafar ɗaukacin nahiyar Afirka.
A makon jiya ne, Kotunan Ɗaukaka Ƙara suka yanke hukuncin soke nasarar gwamnoni uku na jihohin Filato, da Zamfara, da Kano, dukkansu a arewacin ƙasar. PDP ce ke mulki a jihohin Zamfara da Filato, yayin da NNPP ke mulkin Kano.
Hukuncin kotunan ya bai wa hukumar zaɓe ta INEC umarnin ƙwace shaidar cin zaɓe daga hannun Gwamnan Filato Caleb Mufwang, kuma ta bai wa Nentawe Goshwe na APC.
A Zamfara kuma, kotun ta ɗaukaka ƙara ta soke halascin zaɓen Gwamna Dauda Lawal Dare na PDP tare da bayar da umarnin a sake zave a wasu ƙananan hukumomi na Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.
PDP ta ce akwai wasu hujjojin da ba su kai waɗanda ta gabatar ƙwari ba a baya, amma kuma yanzu aka yi watsi da su a shari’o’in da ta kai.
“A gwamnatinmu ta PDP (a baya) an sauke wasu gwamnoni bisa hujjojin da ba su ma kai waɗanda muka gabatar muni ba (a yanzu), amma kuma aka yi watsi da su,” kamar yadda Ibrahim Abdullahi ya bayyana.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta musanta zargin, tana mai cewa “shure-shure ne da ba shi hana mutuwa”.
“Shari’ar nan ba a ɗaki aka kulle aka yanke hukunci ba, alƙalai ne suka yi aiki da hankali da kuma abin da shari’a ta ce,” a cewar kakakin APC na Ƙasa Bala Ibrahim.
Ce-ce-ku-cen na zuwa ne yayin da magoya bayan gwamnan Filato suka hau tituna don gudanar da zanga-zangar nuna qin amincewa da hukuncin kotun a birnin Jos ranar Lahadi.
Wasu masana shari’a a Nijeriya sun soki shari’o’in na Kano, Zamfara, da Filato. Daga cikinsu akwai ƙwararren lauya Femi Falana, wanda ya nemi a sake duba hukuncin.
Kazalika, rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta yi gargaɗin hukunta “masu shirin shirya zanga-zanga bayan samun wasu bayanai da ke nuna cewa wasu qungiyoyin magoya bayan jam’iyyu na yunƙurin shiryawa domin nuna ɓacin rai kan hukuncin kotun”.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC nasara a zaɓen gwamnan jihar Kano, inda ta soke nasarar gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
Hukuncin kotun ya ce Abba bai cancanci zama ɗan takarar gwamna ba, saboda shi ba ɗan jam’iyya ba ne.
