Kowa ya zarce a zaɓen gwamnan Bayelsa, Imo da Kogi

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa zaɓen da ya gudana a ƙarshen mako ya zama zarcewa da kowace jam’iyya da ke kan gado a jihohin. Gabanin shiga zaɓen, mun yi bayani a makon jiya na yadda a ka fara har jihohi 7 su ka zama waje da sauran jihohi a lokacin gudanar da babban zave.

Sakamakon shari’un kotu su ka sauya lokutan zaɓen jihohin. Yanzu ma ba abun mamaki ba ne waɗanda ba su gamsu da sakamakon zaɓen ba su sake garzayawa kotu don neman a yi sabon lale. Nan gaba ma akwai zaɓen gwamnan jihar Edo da Ondo.

Abun fata a nan shi ne kama daga hukumar zaɓe, jami’an tsaro zuwa kotuna su riƙa aiki bisa bin doka da oda ko a wasu kalmomin a ce su tabbatar da adalci musamman a lamuran zaɓe. Ba lalle ne masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi wanda ya cancanta ba don zai iya yiwuwa wani ya canja ko kuma ya gamsar da masu zabe da alƙawuran ƙarya.

Duk da haka matuƙar ƙuri’a na aiki ko kotu na tabbatar da adalci to za a samu gyara don tsarin dimokraɗiyya ba mulki ne na rai da mutuwa ba. Duk mai riƙe da sashen zartarwa ko ya na adalci ko akasin haka to iya tsawon wa’adi shi ne shekara 8 kan karaga ko kuma a samu rabi na shekaru 4.

Ga yadda zaɓen jihohin uku ya gudana ba wata jam’iyya da ta yi asarar jihar ta sai dai ba a san me zai faru a kotu ba. Hakanan wani lamarin ubangiji da ba za a sani ba zai iya sauya zaven in an yi misalign yanda Abubakar Audu ya lashe zaɓe a jihar Kogi amma gabanin a rantsar da shi sai Allah ya yi ma sa rasuwa.

Bayan duba lamarin maimakon tunanin sanya mataimakin sa a takarar James Falake baya sai a ka ɗauko wanda ya zo na biyu a zaven fidda gwani na APC wato wannan gwamna mai baring ado Yahaya Bello a ka ba shi takarar kuma ya yi mulki har wa’adi biyu.

Sai kuma a 1999 inda Atiku Abubakar ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa amma sai Olusegun Obasanjo ya ɗauko shi a matsayin mataimaki inda hakan ya ba wa mataimakinsa tsohon gwamnan Adamawa Bony Haruna damar zama gwamna. Mu ma leƙa abun da ta faru a jihar Zamfara a 2019 inda Mukhtar Shehu Kogunan Gusau na APC ya lashe zaɓe amma rikicin cikin gida ya sa su Kabiru Marafa su ka maka jam’iyyar ƙara ko kuma a ce tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari a kotu da nuna ba a gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’ida ba.

Hukuncin Kotun Ƙoli ya yi awun gaba da Kogunan Gusau da duk wasu zavavvu a inuwar APC inda a ka ba da dama ga ’yan takarar jam’iyya ta biyu mafi yawan ƙuri’a sum aye gurbi da hakan ya sa ’yan PDP su ka kwashi garabasa ko su ka hau mulki a Bello Badum cikin yanayi na bagas.

Tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle Maradun ya zama gwamna amma ba a daɗe ba ya yi wuf ya sauya sheka zuwa APC wanda matakin inji wasu masu sharhi ya yi tasiri a wani ɓangaren na faduwar sa zaɓen tazarce inda har ila yau dan PDP da ya watsar wato Dauda Lawal Dare ya samu nasarar hayewa madafun ikon Jihar Zamfara. Matawalle ya ɗan samu tudun dafawa tun da shugaba Tinubu ya naɗa shi ƙaramin ministan tsaro.

Gwamnan Jihar Kogi mai barin gado Yahaya Bello na APC ya yi nasarar ɗan takarar sa Usman Ododo ya lashe zaɓen gwamnan jihar kamar yadda hukumar zaɓe ta ayyana.

Ododo dai ba ya ga kasancewar sa na gaban goshin Bello a gwamnatin da ke barin gado kazalika ɗan uwan Yahaya Bellon ne.

Wani abun dubawa ɗan takarar PDP wanda ya yi suna a dandalin siyasar PDP mai adawa a taraiya Dino Melaye na uku ya zo a zaven da ƙuri’u dubu 46 inda matashi Murtala Ajaka na SDP ya yi ma sa fintinkau da zuwa na biyu da ƙuri’u fiye da dubu 256.

Yanzu dai za a jira a ga ko in an ƙaddamar da kotun sauraron karar zaɓe ‘yan takarar na adawa za su ƙalubalanci zaɓen ne ko kuwa a’a.

Gagarumin rinjayen da gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi a zaɓen gwamnan jihar ya ba da mamaki kasancewar a zaɓen baya da ya zo na 4 sai da ya garzaya har kotun koli kafin ya samu nasara, inda har a ke yi ma sa gatse cewa shi gwamnan Kotun Qoli ne.

Uzodinma da a ka tabbatar ya na iya aiki da kuɗi wajen cimma burin sa na siyasa, ya samu nasarar a dukkan ƙananan hukumomin jihar.

Hakanan rashin jituwar sa da manyan ‘yan siyasar jihar irin tsohon gwamna Rochas Okorocha da ma wanda ya ƙalubalanta a baya tsohon gwamna Emeka Ihedioha ya sa an zaci ko zai sha da kyar a zaɓen in ma bai sha ƙasa ba.

Gaskiya bayanan sun nuna ba a fito zaɓen yadda ya kamata ba don a wata mazaɓar baya fin kashi 10% ne su ka fito don kaɗa ƙuri’ar su. Fargabar kai hari ma daga ’yan ta’addan IPOB na Biyafara ka iya firgita wasu masu kaɗa ƙuri’a su yi zaman su a gida.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya samu nasarar tazarce a zaɓen da a ka gabatar a ƙarshen mako.

Diri na jam’iyyar PDP ya samu nasara kan babban abokin hamaiyarsa Timipre Sylva na APC.

Dama an yi hasashen Diri ka iya lashe zaɓen tun nasarar sa a ƙananan hukumomi 6 cikin 8 na jihar.

Diri dai na hannun daman tsohon gwamnan jijar ne Seriake Dicson.

‘Yan PDP na ta murna saboda damar cigaba da riƙe madafun iko a jihar Bayelsa. In za a tuna Douye Diri ya samu ɗarewa madafun ikon cikin Bayelsa ne bayan soke zaɓen David Lyon na APC wanda a na jajiberin rantsar da shi sai kotu ta samu mataimakin sa da laifin mika takardun bogi a takarar don haka ta soke zaɓen gaba daya da ba wa jam’iyya ta biyu mafi yawan ƙuri’a dama ta kawo ɗan takarar kuma a rantsar da shi ya zama gwamna.

Nan a ka samu Diri na PDP ke zama na biyu mafi yawan ƙuri’a a zaɓen don haka a ka rantsar da shi inda tsohon gwamna Dickson da muƙarraban sa su ka yi ta murna don hakan nasara su ka samu kan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan wanda ya watsar da PDP ya marawa ɗan takarar APC baya. An tabbatar a lokacin ɗanyen ganye da Jonathan ke yi da tsohon shugaba Buhari ya sa shi juyawa jam’iyyar da ya yi mulki a inuwar ta baya ya mara baya ga ɗan takarar jam’iyyar da ta kayar da shi a 2015.

Allah mai iko David Lyon har fadar Aso Rock a ka kawo shi don gaisawa da shugaba Buhari inda a ka yi ta murna amma ashe murnar za ta koma ciki don kotu ta kawar da shi daga damar zama gwamna.

Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin jam’iyyar AA Olayinka Braimoh ya ce ‘yan sanda sun kulle shi da ‘yan tawagar sa a ɗakin tsare masu laifi har a ka kammala zaɓen jihar.

Braimoh na magana ne da manema labaru labaru a mahaifar sa Kabba inda ya ce ya gamu da akasin ne a kan hanyar sa daga Lokoja yayin da da ya kama hanyar Kabba-Obajana. Duk nasarar ficewa daga dandazon manyan motoci a kan hanyar sai su Braimoh su ka faɗa tsautsayi a wani shingen binciken motoci ko kamar yadda labari ya nuna wata motar jami’an tsaro ta sha kan su don haka su ka tsaya don jin me ya jawo hakan.

Ɗan takarar ya ce samun wata takardar ilmantarwa yadda a ke kaɗa ƙuri’a kuma an rubuta a jikin ta ƙarara cewa ta koyar da kaɗa ƙuri’a ce ta sa ‘yan sandan kama su da kulle su kuma ciki har da ‘yan sandan da ke yi ma sa rakiya.

Ɗan takarar ya ce ba wani sharhi da zai yi kan zaɓen don shi ma bai san wace waina a ka toya ba.

Da farko magoya bayan sa sun firgita don zaton ko sace shi a ka yi gabanin samun labarin ya na hannun ‘yan sanda.

Shin Braimoh zai rungumi ƙaddara ko zai ɗauki matakin shari’a kan akasin ba mu sani ba ko mu ce ba mu samu sabon labari zuwa rubuta wannan shafi na ALƘIBLA ba.

Kammalawa;

Yanzu wannan zaɓe na jihohi uku ya kammala da bayyana sakamako inda gwamnoni biyu masu neman tazarce Hope Uzodinma na Imo da Douye Diri na Bayelsa su ka samu nasarar zarcewa yayin da shi kuma Yahaya Bello mai Abarin gado na Kogi ya yi nasarar ɗan takarar sa Usman Ododo ya lashe zaɓe.

Adalci ga al’ummar jihohin shi ne abun fata sannan in an buɗe kotun qarar zave wanda bai gamsu ba ya shigar da ƙara. Ba amfanin zubar da jini don lamarin zaɓe. An firgita gabanin gudanar da zaɓen don aƙalla mutum uku sun rasa ran su. Tambaya a nan ina amfanin baɗi ba rai?