Zaɓen ƙananan hukumomi: APC ta lashe dukkan ƙananan hukumomin Neja 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi a zaben da aka gudanar a ƙananan hukumomi 25 na jihar Neja.

Haka kuma jam’iyyar ta lashe kujerun kansiloli 271 daga cikin 274 da ake takara a fadin kananan hukumomin, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta samu kujeru uku kacal – biyu a karamar hukumar Tafa da daya a Rafi.

An gudanar da zaɓen ne a ranar 1 ga Nuwamba, inda fiye da jam’iyyu 10 suka tsaida ‘yan takara don neman mukamai daban-daban. Cikin jam’iyyun da suka shiga zaben akwai PDP, APGA, ADC, Labour Party, SDP da Zenith Labour Party, da sauransu.

Kwamishinan harkokin gudanarwa na hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja (NSIEC), Mohammed Liman, ya fitar da sanarwar sakamakon zaben a daren Litinin, inda ya bayyana cewa za a raba takardun shaidar nasara ga wadanda suka lashe zaben.

“Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta jihar Neja (NSIEC) tana sanar da jama’a cewa zaben shugabannin kananan hukumomi na shekarar 2025 an gudanar da shi yadda doka ta tanada a dukkan kananan hukumomi 25 na jihar.

“Hukumar ta kuma tabbatar da cewa dukkan jami’an tattara sakamako sun kammala tattarawa da bayyana sakamako bisa tanadin dokar zabe da ka’idojin aiki na hukumar.

“Bayan nazari da tantancewa, hukumar ta amince da kuma tabbatar da sakamakon kamar yadda jami’an tattara sakamakon suka sanar,” inji hukumar NSIEC.

By ukarofi