Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce ficewar dan majalisa Abdulmuni Jibrin Kofa zuwa jam’iyyar APC da kuma Amb. Oluremi Oguntoyinbo zuwa jam’iyyar PDP ta faru ne sakamakon zagon ƙasa da cin amana da Sanata Rabiu Kwankwaso ya aikata.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin martaninta kan sauyin sheka da wasu daga cikin mambobinta suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP.
A tuna cewa, Kofa, a ranar Litinin, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Haka kuma, tsohon ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar Ogun, Oguntoyinbo, ya bayyana murabus ɗinsa daga jam’iyyar NNPP a ranar Litinin din sannan ya koma jam’iyyar PDP.
A wata sanarwa da Sakataren ƙasa na NNPP, Dakta Ogini Olaposi, ya fitar a yau Talata, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta addabi jam’iyyar na da nasaba da rikicin shugabanci da za a iya kaucewa, wanda Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, da ƙungiyar da ta Kwankwasiyya su ka haifar.
Ya nuna takaici cewa akwai tarin shari’o’i da NNPP ke fuskanta, inda ya kara da cewa “kuma har yanzu ta na fama da rikicin shugabanci, lokacin da Kwankwaso da kungiyar sa suka yi ƙoƙarin karɓe shugabanci da tsarin jam’iyyar.”
“Da dama daga cikin jiga-jigan mambobinmu a Kano sun bar jam’iyyar zuwa APC.”
Olaposi ya bayyana cewa jam’iyyar na sa ran sabon shugabancin hukumar INEC zai gaggauta warware rikicin shugabancin NNPP domin jam’iyyar ta samu damar shiga zaɓukan shekarar 2027 da na gaba yadda ya kamata.
