Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwankwaso ya buƙaci haɗin kai tsakanin Nijeriya da Amurka, ya yi kira ga Tinubu ya naɗa Jakadu da za su rika kare muradun Nijeriya a ƙasashen duniya
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Legas ta ce a shirye jam’iyyar take ta sake ƙwace mulki a Kano a 2027 duk kuwa da sauyin sheƙar gwamnanta tilo Abba Yusuf zuwa jam’iyyar APC.
Sakataren yaɗa labaran NNPP a jihar, Richard Benson, ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Talata a jihar Legas.
A yayin da yake mai da martani kan sauyin sheƙar gwamna Abba, Benson ya ce, “Ya tafi mana, ba zai shafi jam’iyyarmu ba. E, mu yi rashin sa, amma ba zai shafi jam’iyyarmu ba.”
“Zan iya ba ka tabbacin abu ɗaya, a 2027, za mu ƙwace Kano. Ya je mana. Muna da tabbacin ƙwace jihar.
“Mu ba gwamnati ce ƙarfinmu ba, ƙarfinmu shi ne tafiyar Kwankwasiyya.”
“Wannan tafiya ta canja al’amura da yawa a Kano kuma nuna nan da ƙarfinmu. Don haka, ya je abinsa,” ya faɗa.
A cewarsa, tarihi ne ne zai sake maimaita kansa a zaɓen gwamna a 2027 inda NNPP ta kayar da gwamna mai ci a 2023.
“Za mu sake rubuta tarihi” ya faɗa.
NAN ta rawaito cewa Abba ya sauya sheƙa ne a ranar 23 ga watan Janairun zuwa APC tare da mafi yawancin kwamishinoninsa da kuma ‘yan majalisun tarayya da na jiha a NNPP.
Dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44 da mataimakansu da kansiloli waɗanda duk suka koma APC.
