2027: Yankin Kudu maso Yamma zai yi wa Tinubu ruwan ƙuri’u miliyan 10 – Bamidele

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce Jam’iyyar APC ta tsara shirin tattara ƙuri’u domin tabbatar da cewa yankin Kudu maso Yamma ya bai wa Shugaba Bola Tinubu aƙalla ƙuri’u miliyan 10 a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027.

Bamidele ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti na 2026 mai mambobi 57 a birnin Ado Ekiti, babban birnin jihar. Shi ne shugaban wannan kwamitin.

Yankin Kudu maso Yamma ya ƙunshi jihohin Ekiti, Ondo, Ogun, Osun, Lagos da Oyo, kuma Shugaba Tinubu ya fito daga wannan yanki.

Bamidele, wanda ke wakiltar mazabar Sanatan Ekiti ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya ce sake zaɓen Gwamna Biodun Oyebanji a ƙarƙashin tutar APC zai kasance abu mai sauƙi ga jam’iyyar.

Ya amince cewa aikin da ke gaban APC “babba ne”, yana mai cewa shirye-shiryen ba wai kawai don sake zaɓen Oyebanji ba ne, har ma da babban zaɓen 2027.

“Ba wai sake zaɓen Oyebanji kaɗai ba ne. Har ila yau, yana da alaƙa da babban zaɓen ƙasa wanda za a gudanar tsakanin 16 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairu 2027. Wannan batun yana da nasaba da makomar babbar jam’iyyarmu a jihar da kuma a ƙasa baki ɗaya.

“A matsayinmu na jam’iyya mai manufa da hangen nesa, mun riga mun sanya buri kafin zaɓen 2027. Mun tsara shirin tattara kuri’u domin samar wa Shugaba Bola Tinubu, GCFR, aƙalla kuri’u miliyan 10 daga jihohi shida na Kudu maso Yamma kaɗai.

“A matsayin shugabannin APC, yanzu alhakin ya rataya a wuyanmu mu wayar da kan ‘ya’yan jam’iyya da maƙwabtanmu domin su yi rajista a shirin sabunta rajistar masu zaɓe (Continuous ɓoter Registration) da ke gudana.

“Duk da cewa jihar Ekiti na da yawan jama’a kusan miliyan 3.8, adadin masu rajistar zaɓe ya kai 987,647 kawai bisa bayanan 2023.

“Da yake zaɓe na gabatowa, dole ne mu ƙarfafa ‘ya’yan jam’iyya, maƙwabta da dangi su yi rajista a matsayin sabbin masu zaɓe tare da karɓar katin zaɓe na dindindin (PɓC) domin su iya kaɗa kuri’a a zaɓe mai zuwa,” inji shi.

Bamidele ya ƙara da cewa zaɓen gwamnan Ekiti na musamman (off-cycle) da aka shirya gudanarwa a 20 ga Yuni zai zama wata dama ta tabbatar da goyon bayan jama’a ga shugabancin Mista Oyebanji a jihar.

A cewarsa, gwamnan “ya jagoranci jihar da ƙwazo da hangen nesa, tare da haɗin kai da jajircewa wajen inganta rayuwar mazauna jihar da suka haura miliyan 3.8.”

Oyebanji ya gargaɗi magoya baya kan yawan kwarin gwiwa

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Biodun Oyebanji ya gargaɗi ‘ya’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki da su guji yawan kwarin gwiwa, yana mai kira gare su su tunkari zaɓen kamar su ne ke neman cin nasara daga baya.

By ukarofi