Shirin ‘Renewed Hope’ na Tinubu ga ‘yan Nijeriya yaudara ce – Aregbesola

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya ce, shirin shugaba Tinubu na sabunta fata ba zai kawo wa ‘yan Nijeriya wani ci gaba ba.

Aregbesola, tsohon gwamnan Osun ya yi wannan kalamai ne a yayin da yake magana a lokacin gangamin taron jam’iyyar na ƙasa wanda tsagin shugabancin da David Mark yake jagoranta a Abuja.

Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi tsakatsantsan, yana mai cewa gwamnatin ta gaza wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi ba.

“Shirin sabunta fata yaudara ce. Yaushe za a cimma shirin sabunta fatan?” ya tambaya.

Shirin “sabunta fata” babban take ne da shugaba Tinubu ya yi amfani da ita wajen yaƙin neman zaɓensa a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Muhimman alƙawuran da ya yi sun haɗa da: samar da wutar lantarki da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da inganta kiwon lafiya da kyakkyawan yanayin kasuwanci.

Mista Aregbesola ya soki shugaban ƙasa da gaza samar da tsayayyiyar wutar, yana mai cewa har yanzu gwamnatin ta gaza cika alƙawarin.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su gujewa zaɓen gwamnatin a shekarar 2027 saboda gaza cika alƙawarin da ya ɗauka.

Jam’iyyar ADC ta nuna damuwarta game da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya wanda ke nuna gazawa a fannin ilimi.

Jam’iyyar ta yaba wa shugabancin Mark, tana mai cewa jam’iyyar a ƙarƙashinsa ta bunƙasa a cikin watanni 9 inda ta zama babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya.

Mista Aregbesola ya soki hukumar INEC, na ƙin sa ido kan gangamin taronta na ƙasa da take yi.

A cewarsa, hukumar ba ta bayar da gamsasshiyar hujja ba kan matakin da ta ɗauka, yana mai cewa hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi koɗan bai ba ta ikon ɗaukar irin wannan mataki ba.

Ya zargi INEC da zama karen farautar APC domin matsawa wa jam’iyyar ADC, yana mai zargin hukumar da nuna son kai.

By ukarofi