Nijeriya ta zama tamkar ƙasar da ake yaƙi saboda matsalar tsaro — ACF

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta ce matsalar rashin tsaro a Nijeriya ta kai matakin da ƙasar ta zama tamkar ana yaƙi.

Ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki tsaro a matsayin matsala mafi muhimmanci cikin gaggawa.

An bayyana hakan ne bayan taron shugabannin ACF ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Bashir Dalhatu.

Sun ce rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar, musamman a Arewa, sun wuce ƙananan hare-hare, sun koma manyan matsaloli masu barazana.

ƙungiyar ta yi nuni da hare-haren baya-bayan nan a jihohin Borno, Kaduna, Katsina da Binuwai, inda aka kashe mutane da dama tare da raba wasu da muhallansu.

ƙungiyoyin ’yan ta’adda kamar Boko Haram da ISWAP ma sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji, inda suka kashe sojoji da fararen hula.

A cewar ACF, matsaloli kamar tayar da ƙayar baya, fashi da makami, sace mutane da rikicin manoma da makiyaya sun haɗu sun zama babbar barazana ga ƙasa, wanda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

ƙungiyar ta ce mutane da dama sun mutu ko kuma sun bar gidajensu, yayin da magidanta suka shiga mawuyacin hali.

Ta kuma yi gargaɗin cewa rashin tsaro na shafar noma, wanda ke jawo ƙarancin abinci da hauhawar farashi.

ACF ta bai wa gwamnati shawarar ɗaukar matakin irin na lokacin yaƙi, ta hanyar mayar da hankali kan tsaro tare da rage kashe kuɗi kan abubuwan da ba su da muhimmanci.

Ta jaddada cewa ba za a samu ci gaba ba idan babu tsaro.

Tsohon sakataren ACF, Anthony Sani, ya ce gwamnati kada ta dogara da ƙarfin soji kawai, sai ta kuma magance tushen matsalolin kamar talauci, rashin aikin yi da rashin ilimi.

ƙungiyar Afenifere, ita ma ta nuna damuwa kan yawaitar hare-hare a yankin Kudu maso Yamma, tare da kira ga gwamnoni su ɗauki mataki mai tsauri.

Ta kuma buƙaci a ƙara wa hukumomin tsaro kayan aiki da goyon baya, tare da gargaɗin cewa wasu mutane a cikin al’umma na taimaka wa masu laifi.

Wani tsohon babban jami’in ’yan sanda, Adisa Bolanta, ya buƙaci a ayyana dokar ta-ɓaci kan rashin tsaro, tare da ƙara kuɗi da gyara tsarin aikin ’yan sanda da sojoji.

Ya ce dole ne a kai kayan aiki da tallafi ga jami’an da ke aiki a filin daga domin inganta tsaro a ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi