Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wakilan ofishin jakadancin Birtaniya a Nijeriya sun halarci babban taron jam’iyyar ADC da ɓangaren da David Mark ke jagoranta ya shirya a ranar Talata.
Haka kuma, jakadan ƙasar Sin a Nijeriya, Yu Dunhai, ya halarci taron da aka gudanar a Rainbow Event Centre da ke Abuja.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa na ɓangaren, Rauf Aregbesola, ne ya tabbatar da halartar wakilan ƙasashen biyu.
Ofishin jakadancin Birtaniya ya samu wakilci ne daga tawaga mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin sakataren siyasa, Thomas Samson, yayin da wata ma’aikaciyar ofishin, Damilola Oyedele, ta kasance cikin tawagar.
Bayan fara taron, tsohon Sanata Dino Melaye, wanda ke jagorantar shirin taron, ya sanar da isowar jakadan ƙasar Sin, yana mai cewa an samu ɗan tsaiko a sadarwa sakamakon bambancin harshe.
Halartar jakadun ƙasashen waje ba abin mamaki ba ne, domin ɓangaren da David Mark ke jagoranta ya sha roƙon al’ummar ƙasa da ƙasa su sa ido kan rikicin shugabancin jam’iyyar.
ɓangaren ya gudanar da taron duk da cewa Independent National Electoral Commission (INEC) ta janye amincewarta da shugabancinsa makonni biyu da suka gabata.
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na ranar 12 ga Maris, wanda ya shafi halaccin shugabancin ɓangaren David Mark. INEC ta kuma bayyana cewa ba za ta yi mu’amala da wani ɓangare na daban ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala ba.
A halin yanzu, jam’iyyar ADC ta kasu gida uku masu fafatawa kan iko kafin zaɓen 2027. Baya ga bangaren Mark, akwai ɓangaren Nafiu Bala da kuma sabon bangaren Dumebi Kachikwu, wanda shi ma ke iƙirarin shi ne halastaccen shugabanci.
Wannan sabon ɓangare ya yi watsi da ɓangarorin Mark da Bala, yana zarginsu da kwace ikon jam’iyyar, tare da goyon bayan matakin INEC na janye amincewa. Sun kuma buƙaci a kafa kwamitin rikon kwarya na tsaka-tsaki domin tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Dukkan bangarorin sun nuna rashin amincewa da matakin, inda kowanne ke dagewa cewa shi ne sahihin shugabancin jam’iyyar.
Bangaren Mark ya kuma bukaci shugaban INEC, Joash Amupitan, da sauran kwamishinonin ƙasa da su yi murabus.
