Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗan takarar Shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Peter Obi, ya bayyana cewa zai iya ficewa daga jam’iyyar idan aka samu matsala ko magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar dai ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja a ranar Talata.
Obi, wanda shi ne dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya bayyana haka ne a daren Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Arise News Prime Time.
Mai gabatar da shirin, Charles Aniagolu, ya tambaye shi kan zargin da ake masa na yawan sauya jam’iyya maimakon gyara matsalolin cikin gida.
Sai dai Obi ya kare kansa, yana cewa duk lokacin da ya bar wata jam’iyya, ya yi hakan ne saboda kin amincewa da rashin gaskiya da maguɗi a zaɓen fidda gwani.
Ya ce ya bar jam’iyyar APGA ne saboda matsalolin wariya da ya ce ya fuskanta daga magajinsa, Willie Obiano.
Haka kuma, ya ce ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa LP ne saboda rashin bin ƙa’idoji da kuma yadda aka mayar da zaɓen fidda gwani kasuwanci.
“Ba zan iya shiga zaɓen da ake saye da kuɗi ba. Ba zan biya mutane kuɗaɗe domin su yi min aiki ba,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko zai fice daga ADC idan irin wannan matsala ta sake faruwa, Obi ya ce zai ɗauki irin wannan mataki ba tare da wata shakka ba.
“Ko da zan yi hakan sau 20, zan yi — zan bar ADC. Ba zan shiga abin da aka lalata ba. Ba zan iya cewa ina son canji ba alhali ina cikin tsarin da ba shi da gaskiya,” ya bayyana.
Ya ƙara da cewa duk da cewa yana tare da wasu tsoffin ‘yan PDP da suka koma ADC, idan aka sake samun matsala a tsarin zaɓen fidda gwani, zai fito fili ya yi magana.
A wani ɓangare, Obi ya zargi gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da hannu a rikicin shugabanci da ya raba jam’iyyar LP gida biyu.
Ya ce ya yi mamakin yadda hukuncin Kotun ƙoli na watan Afrilu 2025, wanda ya kori shugabancin Julius Abure, bai samu cikakken aiwatarwa daga hukumar zaɓe ba sai bayan kusan watanni takwas.
A ƙarshe, INEC ta amince da Nenadi Usman a matsayin shugabar jam’iyyar.
Obi ya ce an haddasa rikicin ne domin daƙile burinsa na zama shugaban ƙasa.
“Sun kunna wuta a LP domin su hana ni. Amma na fita daga cikinta,” inji shi.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta sha musanta zargin cewa tana da hannu a rikicin jam’iyyar.
