‘Yan bindiga sun kashe Sakataren PDP a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ɓarayin daji ne a Jihar Zamfara, sun kashe Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙaramar Hukumar Tsafe a jihar, Musa Ille.

Majiyarmu ta ce an kashe marigayin ne a ƙofar gidansa bayan da da ‘yan bindigar suka yi wa gidan ƙawanya a ranar Litinin da daddare.

Shugaban PDP na yankin, Garba Garewa, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce, “Muna zargin makisan ‘yan fashin daji ne, jiya (Litinin) suka shiga gidansa suka halbe shi.”

Wani mazaunin yankin, Abubakar Tsafe, ya shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa, bayan da ‘yan bindigar suka shiga yankin sai suka kira sakataren kan ya fito ya duba wani abu a bayan gidansa.

Ya ci gaba da cewa, haka dai Ille ya fito waje ba tare da sanin cewa su ɗin ‘yan bindiga ne ɗauke da makamai ba.

Sai dai, ya zuwa kammala haɗa wannan rahoto babu wani bayani daga ɓangaren hukumomi kan batun a jihar.