NDLEA ta damƙe masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi 51,000, ta gurfanar da 9000 a cikin shekara uku

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta ce a tsakanin shekaru uku da suka gabata, ta samu nasarar damƙe masu ta’ammali da miyaƙun ƙwayoyi mutum 50,901 kana ta gurfanar da 9000.

Shugaban Hukumar na Ƙasa, Buba Marwa ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamarwa da kuma miƙa ginin da Gwamnatin Birtaniya ta bai wa hukumar a matsayin gudunma wanda aka gudanar a ranar Litinin.

Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ta rawaito Marwa na cewa, daga cikin mutum 50,901 da aka kama bisa zargin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin, an gurfanar da 9,034 inda suka fuskanci hukunci daidai da laifukan da suka aikata.

Ta ƙara da cewa, hukumar ta samu nasarar kama miyagun ƙwayoyi sama da ton 7,561 a tsakanin watanni 38 da suka shuɗe.

Kazalika, sanarwar ta ce Marwa ya aike wa masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyin saƙon cewar, Nijeriya ba za ta lamunci miyagun ayyukan da suke aikatawa a cikin ƙasa ba, don haka su tuba su daina ko kuma su gamu da fushin hukuma.

Ya ce, sakamakon shirin bincike da yaƙi da yaƙi da miyagun ƙwayoyin da suke gudanarwa, sun kama tare da lalata gonakin tabar wiwi kadada 1,057.33348 a cikin shekarun ukun da suka gabata.

Daga nan, Marwa ya yaba tare da jinjina wa Gwamnatin Birtaniya bisa gudunmawar da ta bai wa hukumar.

A ƙarshe, ya ce, NDLEA ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da fatattakar masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a sassan Nijeriya.