Shugabancin APC na Jihar Kano ya dakatar da waɗanda suka dakatar da Ganduje a matakin Gunduma

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar APC na Jihar Kano, ya saka wa shugabannin jam’iyyar na gundumar Ganduje c’da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa takunkumi bisa dakatar da Shugaban APC na Ƙasa Umar Abdullahi Ganduje, da suka yi a ranar Litinin.

Shugabancin APC na ƙaramar hukumar ya daƙile matakin dakatarwar da aka yi wa Gandujen ne tare da sauke waɗanda ke da hannu a korar daga muƙamansu.

Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Inusa Dawanau, ya shaida wa manema labarai cewa, an samu waɗanda suka dakatar da Ganduje da yi jam’iyya zagon ƙasa, tare da cewa an samu bayanai kan yadda suka yi tarurruka tare da ‘yan jami’yyun hamayya a lokuta daban-daban.

Bayan amincewa da takunkumin da aka ƙakaba wa waɗanda lamarin ya shafa, Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya kuma ce ya dakatar da su daga shiga harkokin jam’iyyar na tsawon wata shida.

Haka nan, ya ce an kafa kwamiti na musamman don gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa waɗanda lamarin ya shafa.

A nasa ɓangaren, Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce tuni uwar jam’iyyar ta jiha ta amince da matakin da shugabancin jam’iyyar na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya ɗauka kan batun bisa ƙwararan hujjojin da aka gabatar.