Raɗɗa ya raba wa jami’an tsaro motocin aiki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya miƙa wa jami’an tsaro motocin yaƙi masu sulke guda 10 domin gudanar da aiki a ƙananan hukumomi takwas dake fama da matsalar rashin tsaro a jihar Katsina don ƙarfafa tsaron al’uma.

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da motocin ne don inganta tsaron jihar wanda sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron da gwamnatin jihar ta kafa ke jagoranta a ƙananan hukumonin da matsalar ta fi ta’azzara.

Taron miƙa motocin ya gudana ne ranar Talata a gidan gwamnatin jihar.

A jawabinsa, Gwamnan ya nanata cewa zai ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro don ganin an samar wa hukumomi tsaro da suka haɗa da, Katsina Community Watch Corps da ‘yan Sanda, sojoji da aikin da ya dace domin fuskantar matsalar rashin tsaro a jihar Katsina.

Ya kuma bayyana cewa, samar da motacin na ɗaya daga cikin alƙauarian da ya yi wa al’umar jihar lokacin yaƙin neman zaɓe.

A cewarsa, matsalar tsaro a Katsina ta kusa zama tarihi duba da yadda gwamnatin jihar ke samun tallafi daga Gwamnatin Tarayya don dawo da zaman lafiya a jihar.

Kodayake, ya ce ba za a ce an kawar da rashin tsaro gaba ɗaya a jihar ba, amma ya tabbatar wa da al’ummar jihar cewa an samu gagarumin ci gaba, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da zaman lafiya a faɗin jihar Katsina.

An ware motocin ne ga ƙananan hukumomi takwas da suka fi fama da rashin tsaro da suka haɗa da Safana da Batsari, Ɗanmusa da Ƙanƙara da Faskari da Sabuwa da Ɗandume da kuma ƙaramar hukumar Jibia.