Me ya jawo mutuwar auren G-Fresh da Sadiya Haruna? 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Tun bayan da jarumar Tiktok ɗin nan, kuma tsohuwar matar G-Fresh Al-Ameen, Sayyida Sadiya Haruna ta fitar da sanarwar cewa, aurenta da tsohon mijinta Abubakar Ibrahim (G-Fresh Al-Ameen) ya zo ƙarshe, sakamakon biyansa kuɗi Naira dubu 500 da ta yi, mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu.

Daga masu cewa dama mun san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, sai masu cewa gara ma haka, an sayar da gonar rago an saya mai fura! 

Za ku iya tunawa tun da sanyin safiyar wata ranar 16 ga Yuni na shekarar 2023 ne zaurukan sada zumunta suka wayi gari da hotunan auren waɗannan jarumai biyu, wanda ya jawo cece-kuce, daga wajen jama’a. Har wasu na zargin ko ba gaskiya ba ne, saboda yadda ake ganin shiriritar da suke yi a manhajar Tiktok, ana ganin wasa kawai suke yi, don neman ra’ayin jama’a. 

Amma bayan jaruman sun tafi umara tare kuma sun dawo an shirya gagarumin buki cikin watan Yuli na 2023, wanda ya samu halartar manyan jaruman Kannywood da ƴan Tiktok, jama’a sun yi ta musu fatan alheri, tare da kiran su ba mara ɗa kunya, kada jama’a su yi musu dariya. 

Sai dai watanni ƙalilan da auren nasu sai aka fara ganinsu a rana. Domin kuwa a ranar 28 ga watan Satumba, 2023 sai ga wani labarin da ke cewa, Sadiya Haruna ta maka mijinta G-Fresh a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Kano tana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu.

Jarumar, wacce aka fi sani a TikTok da Sayyida Sadiya Haruna, ta ce ta fahimci cewa mijin nata ba irin wanda take so ba ne, kuma ba za ta iya ƙarasa sauran rayuwarta tare da shi ba. 

Bayanai na nuni da cewa wannan na zuwa ne sakamakon saɓanin da ma’auratan suka samu bisa zargin da G-Fresh ke yi wa matarsa na cigaba da hulɗa da wani namiji, wanda ita kuma ta ce abokinta ne (Besty), shi kuma mijin nata ya ce ba zai lamunci haka ba.

Ita kuma amarya Sadiya Haruna ta ce babu mai rabata da amininta, don kuwa ba za ta iya rayuwa ba sai da shi.

A wasu rahotannin ma cewa aka yi Sayyidar ta hana mijinta kusantarta na tsawon wani lokaci, saboda wai ba ta gama amincewa da ingancin lafiyarsa ba. 

Duk ƙoƙarin da kotu ta yi na ganin ta bai wa ma’auratan damar sasantawa abin ya gagara.

Yayin da ita Sadiya ke cewa ba za ta iya cigaba da zama da G-Fresh ba, shi kuma gogan naku ya ce yanzu ma ya ga mata! 

Zama dai tsakanin waɗannan jarumai ya ƙi daɗi, har ta kai ga an ce G-Fresh ya yi yaji ya bar gidan da suke zaune, zuwa wani waje na daban.

Sai dai su haɗu a zaurukan sada zumunta inda suke aikawa juna saƙonnin tura-haushi na yadda suke gudanar da rayuwarsu, ba kare bin damo.

Yayin da jama’a ke tir da wannan aure nasu, wasu kuwa shawara suke basu kan su rabu da juna kawai, kowa ya kama gabansa. 

Yadda waɗannan jarumai suka riƙa tona asirin zamantakewar aurensu a duniya ya sa jama’a da dama bayyana takaici kan yadda su ke ɗaukar aure ko yadda suke gudanar da wata irin rayuwa ta rashin mafaɗi. 

A wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook, Hajiya Umma Suleiman Ƴan’awaki ta bayyana takaicinta kan yadda auren waɗannan jarumai yake ta tangal-tangal.

A lokacin da shi G-Fresh Al’Ameen ke ƙara jaddada cewa, aurensa da Sadiya na nan daram, ita kuwa Sadiya Haruna ta goge duk wani hotonsu da bidiyonsu da mijin nata ta yi a shafinta na Tiktok, ciki har da na bikinsu. 

Ta ce, “Wasu na ganin wasa suke yi da ƙwaƙwalen mutane saboda su kawar da idon maqiya a kansu. Amma ko ma dai mene ne Allah Ya sani na damu, ba na son auren nan ya mutu. Allah Ya sa min ƙaunarsu, tunda suka yi aure na ji ina son kasancewarsu har abada a matsayin ma’aurata.”

Ganin yadda ake ta yamaɗiɗi da wannan jita-jitar mutuwar auren G-Fresh da Sadiya Haruna, wani mai amfani da zaurukan sada zumunta, Abdul Ibrahim cewa ya yi, “Allah na tuba, ai da wannan haukar da suke yi da sunan aure gwara su jingine auren su huta. Don zaman auren nasu babu tauhidi a ciki daga gore-gore sai tsine-tsine da gulmace-gulmace. Ai dama kowa ya sayi rariya ya san za ta zubar da ruwa.”

Sabi’u Isa Suleiman kuwa cewa yake yi, “Ai abin jin daɗi ne ma a ce auren ya mutu, domin haukar da suke yi a cikin auren samsam zubar da kima da darajar da Allah Ya yi wa aure suke yi.”

Amma shi Kabiru Mazangari fatan alheri yake yi musu, yana mai cewa.

“Masu bin ku da sharri, Allah Ya shiryesu. Ku dai ku sa ido ku yi kallo, sannan ku yi amfani da iliminku. Allah kuma Ya baku zaman lafiya. Mutuwa nake fata ta raba ku, wanda kuma ta zama dole a kan kowa!”

Duk da irin waɗannan maganganu na fatan alheri da tofin Allah-tsine da wasu suka riƙa yi a kan auren nan.

A ƙarshe dai sai da Sadiya Haruna ta tabbatar da auren nan bai ɗore ba, kamar yadda ta sha alwashi.

A ranar 7 ga watan Afrilu na wannan shekara, 2024, da kanta Sadiya Haruna ta fitar da sanarwa kan mutuwar auren nasu, inda ta rubuta cewa, “Yau na karɓi takardar saki daga hannun G-Fresh da ya yi min, bayan na ba shi zunzurutun kuɗi har Naira dubu ɗari biyar. Ina yi masa fatan alheri. Allah Ya haɗa kowa da rabonsa.”

Wannan ce ta kawo ƙarshen cece-kucen da aka ɗauki tsawon watanni ana yi game auren da bai cika ko shekara guda ba.

Addu’armu ita ce Ubangiji Allah Ya sa hakan ya zama sanadiyyar shiryuwarsu, da fatan abin da ya faru ya zama musu darasi, kuma duk auren da za su yi nan gaba su riƙe shi da amana da kulawa.