Kotu ta umurci Jaruma Halima Abubakar da ta biya Apostle Suleman tarar miliyan 10

Daga AISHA ASAS

Babbar Kotun Tarayya ta umurci jaruma a masana’antar Nollywood Halima Abubakar da ta biya tarar Naira miliyan 10 ga Apostle Johnson Suleman kan kalaman ɓata suna da ta yi a shafinta na Instagram.

Baya ga haka, kotun ta haramtawa jarumar yin kowanne irin kalamai kan faston.

Suleman ya zargi jarumar da wallafa kalaman cin zarafi gare shi ciki kuwa har da kiransa da mutumin banza da kuma mabiɗi mata.

Duk da cewa kotun ta ba wa jaruma Halima damar kare kanta tare da bayar da hujjar da za ta wanke ta daga zargin na limamin Cocin, sai dai ta kasa gabatar da komai wanda hakan ya ba shi nasa.

Daga ƙarshe kotun ta nemi jaruma Halima Abubakar da ta janye kalamanta ga Suleman, sannan ta goge duk wani rubutu da ta yi nasa na vata suna a intanet.