An kori Ganduje daga Jam’iyyar APC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar APC ta mazaɓar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta sanar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mamaba a jam’iyyar.

Mai bai wa Jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje, Hon. Halliru Gwanzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin.

Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ta yi masa na karɓar cin hanci da rashawa.

Ya ce dakatarwar ta fara ne daga daga ran 15 ga Afrilu.

Tsohon gwamnan na Kano wanda a yanzu shi ne shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta sanya kwamitin bincikarsa kan zargin cin hanci da rashawa.