Mun samu nasarar taƙaita ayyukan rashin ɗa’a a gidajen wasanni a Kano – Hukumar Tace Finafinai

Daga WAKILINMU

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-mustapha, ta bayya nasarar da ta samu wajen taƙaita ayyukan rashin ɗa’a a gidajen wasanni yayin bikin Ƙaramar Sallah da ya gabata.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, “Babbar Nasarar mu a bana ita ce yadda ayyukan rashin ɗa’a suka ragu a gidajen wasanni yayin bikin Ƙaramar Sallah.”

Ta ƙara da cewa, “Mun yi gargaɗi tare da bada shawarwari ga wasu daga cikin gidajen wasannin a faɗin Kano.

“Kwamitin bin dig-digi kan yadda gidajen wasanni a faɗin Jihar Kano suka gudanar da shagul-gulan bikin sallah wanda Shugaban Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano, Abba El-mustapha ya kafa ƙarƙashin jagoranci Alh. Abdulkarim Badamasi, ya ce, a zagayen da kwamitin ya yi na tsawon kwanaki huɗu cikin sallah bai sami Kowanne gidan wasa da laifin karya doka ba.

“Sai dai, sun yi gargaɗi tare da bada shawarwari ga wasu gidajen wasannin kan yadda za su inganta harkar lafiya, wato samar da wadatacciyar iska domin guje wa kamuwa da cututtuka wanda ke da alaƙa da cakuɗuwar numfashi.

“Haka kuma, kwamitin ya ba wa wasu gidajen wasanni shawara kan yadda za su inganta tsaro ga dukiyoyin al’ummar da ke zuwa kallon wasanninsu a lokaci irin na bikin sallah,” in ju sanarwar.