A karon farko cikin shekaru 120 Bayer Leverkusen ta zama zakaran gasar Bundesliga

Daga IBRAHIM HAMISU

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga na Jamus na shekarar 2023/2024, karon na farko da kafa ƙungiyar shekara 120 da ta gabata, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Nasarar da suka samu ta kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Kazalika Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da mai horaswa Xavi Alonso dan kasar Sifaniya ya karɓe su.