Tinubu ya nuna alhini kan rasuwar Saratu Giɗaɗo

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nuna alhininsa dangane da rasuwar jaruma a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi dani da Daso.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Afrilu da kuma sa hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale.

Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwan da abobakan aiki da masoyan marigayiyar da ke sassa daban-daban.

Tinubu ya bayyana rasuwar jarumar mai shekara 56 a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, mutuwarta ta haifar da wagegen giɓi mai wuyan cikewa a masanantar nishaɗi.

Haka nan, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da ɗaukacin waɗanda suka tasirantu da marigayiya Saratu Guɗaɗo, kana ya yi addu’ar Allah Ya jikanta da rahma.