Alaƙar tattalin arzikin Nijeriya da sharrin Yahudawa da Nasara

Daga ALIYU ƊAHIRU ALIYU 

Da yawan mutane suna ɗauka karyewar darajar kuɗin ƙasa kamar sharrin Amurka ne ko kuma ba abu ne mai kyau ba.

Amma sau da yawa gwamnatoci da kansu suke karya darajar kuɗin ƙasarsu ta hanyar “devaluation”. Me ya sa?

Karya darajar kuɗin yana da matsala ta wata fuskar amma yana da alfanu ta wata fuskar.

Kuma tamkar kowane sha’ani na tattalin arziki, dole zaɓi ne ake yi a tsakanin matsaloli biyu a ɗauki ɗaya a bar xaya (trade-offs). A tattalin arziki ba a jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya. 

Ƙasar da ta karya darajar kuxinta tana saka yan ƙasarta su rage siyo kayan ƙasashen waje saboda zai yi tsada, don su dinga ƙirƙiro na gida, yawan siyo kayan waje matsala ne ga ƙasa.

Don haka hanyar magance hakan shi ne a saka kayan su yi wa ‘yan ƙasa tsada. Idan ‘yan ƙasar suka ji wuya to za su koma cin na gida har ma su koma siyarwa ƙasashen waje su haɓaka tattalin arzikin ƙasar bakiɗaya a gaba. 

Abu na biyu kuma shi ne, karya darajar kuɗin ƙasa yana sakawa idan ana bin ƙasa bashi to ta iya biyan bashin ta samu canji. Irin wannan abin ne Najeriya ta yi.

Tare da cewa za ka ga iya zaton kamar karya darajar Naira zai janyo a biya bashi da tsada, amma a haƙiƙa karya darajar Naira shi ne zai rage yawan bashin da ake bin gwamnati har a samu canjin da za a iya albashi da sauran ayyuka a ƙasa. 

Babban abin da ya sa kuwa ake karya darajar kuɗin ƙasa shi ne idan ana son yan ƙasashen waje su shigo ƙasa su kafa masana’antu. Idan dan Najeriya zai tafi wata ƙasar ya gina masana’anta zai sha wuya saboda kuɗinsa ba shi da daraja.

Amma idan ɗan wata ƙasar zai zo Najeriya zai ga a araha zai gina kamfani saboda darajar kuɗinsa. Ta haka za a zo a samar da aiyukan yi kuma a bunqasa tattalin arzikin qasa. 

To, amma me ya sa talakawa ba sa so a karya darajar Naira? Saboda sun saba da mafi yawan abubuwan da suke amfani da shi daga waje ake kawowa.

Dole abubuwa su yi tsada sosai kafin a samar da na gida. Indomi ta ninka kuɗinta sau wajen huɗu ne saboda da da ake siyo ta. Haka da yawa daga kayan da ake haɗa abubuwa an saba siyo su daga waje ko da kuwa a Nijeriya za a iya samunsu.

Amma wannan wuyar da aka shiga ita za ta taimaka wajen mutane su samo mafita tun da dama an ce “necessity is the mother of invention.”

Aliyu masani ne kuma mai sharhi ne kan al’amurra na yau da kullum musamman waɗanda suka shafi zamantakewar al’umma da siyasa.