Kuɗin lantarki: Ma’aikatan lantarki sun yi barazana shiga yajin aiki a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa ta yi kira da a sake nazari a kan ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi a baya-bayan nan, inda ta yi barazanar shiga yajin aiki.

A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar, Adebiyi Adeyeye, ya yi gargaɗin yiwuwar shiga yajin aikin matuƙar ba a sauya ba.

Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Nijeriya ta kara haraji ga kwastomomin da ke samun wutar lantarki na sa’o’i 20 a kullum, lamarin da ya haifar da ƙarin farashin. 

Adeyeye ya bayyana rashin daidaiton tsarin a matsayin hanyar da ke kashe gwiwar masu dogaro da wutar lantarki don buƙatun su na yau da kullum, musamman marasa galihu.

Da yake zayyana kamanceceniya da sauran ƙasashe, Adeyeye ya bayar da hujjar bayar da tallafin gwamnati kan wutar lantarki, inda ya bada misali da ƙasashe masu cigaba kamar Jamus da Amurka.

Ya kuma jaddada buƙatar ba da fifiko ga walwalar tattalin arzikin ma’aikatan Nijeriya sannan ya buƙaci haɗa kai don ƙalubalantar matakin.

Hukumar ta NUEE ta yi Allah wadai da ƙarin kuɗin, kuma ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa domin sauya shi.

Rashin magance wannan batu na iya haifar da tsauraran matakai, ciki har da janye mambobin da ke da hannu wajen aiwatar da sabon haraji. 

Ƙungiyar ta yi kira ga ɗaukacin ’yan Nijeriya da su ba da haɗin kai wajen ganin an yi adalci tare da samar da wutar lantarki cikin adalci.