Wulaƙanta Naira ta janyo wa ɗan daudu, Bobrisky zaman kuruku na wata shida

Daga BASHIR ISAH

Labarin da muka samu yanzu-yanzu na nuni da cewa, ɗan daudun nan Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky, zai shafe wata shida a kurkuku ba tare da wani zaɓi ba bayan da kitu ta kama shi da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira.

Mai shari’a Abimbola Awogboro na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ce ta yanke wannan hukunci.

Alƙalin ta ce hakan zai zama darasi ga sauran jama’a waɗanda ke da ɗabi’ar wulaƙanta Naira.