’Yan bindiga sun bi Sarkin Musulmi ranar sallah

*Sun miƙe ƙafa a bainar jama’a

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wasu dandazon ’yan ta’addar daji sun miƙe ƙafa a lokacin Ƙaramar Sallah da a ka gudanar ranar Larabar da ta gabata, inda suka fito suka gudanar da sallar idi tare da sauran bukukuwa a bainar jama’a a Jihar Zamfara da ke yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Bikin sallar ’yan bindigar daji ya zo ne a daidai lokacin da wasu malamai su ka bijire wa umarnin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, na sauke azumin watan Ramadan a ranar Laraba.

Sarkin Musulmi ya sanar da cewa, ba a fa jinjirin watan Shauwal ba a ranar Litinin, don haka ya umarci dukkan al’ummar Musulmi a Nijeriya da su cika azumi na 30 zuwa ranar Talata maimakon 29, kamar yadda a ka fi sabawa da hakan.

To, amma an ruwaito wasu malaman addinin Islama su na ƙalubalantar hakan, inda aka ga wani fitaccen malami ya na jagorantar sallar idi a ranar Talata.

To, sai dai kuma bayyanar bidiyon wasu ’yan bindigar daji a Jihar Zamfara su na gudanar da sallar idi a ranar Laraba, ya gwada cewa, sun yi aiki da umarnin Sarki Sa’ad Abubakar kenan.

Wani ƙwararre ta fuskar kwantar da tarzoma da sharhi kan harkar tsaro da ke yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Makama ya ce, ’yan ta’addar sun gudanar da sallar idi ne a cikin garin Munhaye da ke Jihar Zamfara a ranar Laraba biyo bayan kammala azumin watan Ramadan, inda suka nuna halin ko-in-kula game da abinda ka iya zuwa ya dawo daga jami’an tsaro.

A wannan shekara dai, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta qara ranar Alhamis a matsayin kwana na uku, domin yin hutun sallah a madadin kwanaki biyu da ta saba bayarwa domin gudanar da kowaɗanne hidindimun cikin lumana a faɗin ƙasar.

Amma kasancewar Fadar Sarkin Musulmi ta sanar da cewa, ba a ga watan sallah ranar Litinin ba, tilas ta sanya Gwamnatin Tarayyar Nijeriya qari kan ranakun hutu maimakon Talata da Laraba zuwa har Alhamis.

Sai dai hakan da ’yan ta’addan suka yi ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma bisa la’akari da yadda ake fama matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa da ma wasu yankuna na faɗin ƙasar.

Sannan kuma, ɗaukar bidiyon da aka yi ya sake ƙara nuna cewa, har yanzu akwai rashin tsaro ga al’ummar wannan yankin da ma ƙasar bakiɗaya, wanda jami’an tsaro ke cewa su na cigaba da ƙoƙarin magancewa tsawon shekaru da dama.