16
Aug
Daga AISHA ASAS Najeriya da Chana sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da nufin ƙarfafa alaƙa tsakanin masana’antun fina-finai da talabijin na ƙasashen biyu, a wani mataki da ake sa ran zai kara bude kofar musayar fina-finai da kwarewa tsakanin ɓangarorin. An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin Chana Movie Channel da Nigerian Television Authority (NTA) a Abuja ranar Juma’a, yayin taron Chana–Nigeria Film and Literature Symposium. Yarjejeniyar ta ƙunshi shirya fina-finai tare, musayar shirye-shiryen talabijin da fina-finai, horas da kwararru, da kuma musayar fasaha. Haka kuma, ɓangarorin biyu sun amince da faɗaɗa hanyoyin rarraba ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire, lamarin da zai iya…
