Hukumar FCC ta fara bincike kan lasisin tashoshin ABC bayan barkwancin Jimmy Kimmel

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Wani sabon rikici mai nauyi ya kunno kai a duniya nishaɗi, bayan fitaccen mai gabatar da shirin talabijin na Amurka, Jimmy Kimmel, ya tsinci kansa a tsakiyar muhawara mai zafi da ta haɗa gwamnati, kamfanonin watsa labarai da masu kare ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Lamarin ya samo asali ne daga wani barkwanci da Kimmel ya yi a cikin shirin sa na dare, wanda wasu suka fassara a matsayin magana mai nauyi kan shugabannin ƙasa. Wannan ya sa Fadar White House ta fito fili tana kira da a ɗauki mataki a kansa, har ma aka buƙaci kamfanin Walt Disney Company da ke mallakar tashar ABC da ya sallame shi.

Sai dai al’amarin bai tsaya nan ba. Hukumar Federal Communications Commission (FCC) ta shiga cikin lamarin, inda ta fara duba lasisin wasu tashoshin ABC, matakin da masana suka ce yana da matuƙar nauyi kuma ba a saba ganin irinsa ba cikin shekaru da dama.

A nasa ɓangaren, Kimmel ya fito ya kare kansa, yana mai cewa an fassara barkwancinsa ba daidai ba, kuma bai nufin tayar da hankali ko yin wata kira ta tashin hankali. Ya jaddada cewa, abin da ya faɗa barkwanci ne na al’ada a irin waɗannan shirye-shirye.

Sai dai wannan martani bai dakatar da ce-ce-ku-ce ba. Wasu na ganin gwamnati na ƙoƙarin takura ‘yancin faɗar albarkacin baki, yayin da wasu ke ganin dole ne a sanya iyaka ga irin kalaman da ake yi a bainar jama’a.

Masana harkar doka da watsa labarai sun bayyana cewa, wannan rikici na iya zama wani muhimmin gwaji ga tsarin dimokuraɗiyya, musamman yadda ake daidaita ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma alhakin kalamai a bainar jama’a.

By ukarofi