Daga AISHA ASAS
Sabon fim mai suna ‘The Devil Wears Prada 2’ ya zama abin magana a duniya, bayan da aka sake dawo da fitattun jarumai da suka yi fice a kashi na farko tun shekaru kusan ashirin da suka gabata.
Jarumai irin su Meryl Streep da Anne Hathaway sun sake bayyana a cikin rawar da ta ɗaukaka su, lamarin da ya jawo farin ciki ga masoya fina-finai a duniya, musamman a Amurka da Turai.
Rahotanni daga manyan kafafen fina-finai sun nuna cewa a ranar 29 ga Afrilu, 2026 aka fara bayyana cikakkun bayanai da ke nuna yadda fim ɗin ke ƙoƙarin haɗa tsohon salo da sabbin sauye-sauyen zamani a harkar ƙira da rayuwar ma’aikata.
Sai dai duk da wannan farin jini, wasu masu sharhi sun fara bayyana damuwa kan wasu sassan labarin, musamman ɓangaren soyayya da ake ganin bai kai matsayin da ake tsammani ba.
Masana na ganin cewa wannan muhawara da ake yi na iya zama wata hanya da za ta ƙara ɗaga darajar fim ɗin a kasuwa.
