Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi, amma kamar ba su shirya amsar sa ba ne – Muhammad Galadima

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Taron bikin bajekolin finafinai na Afirka wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festiɓal’ wanda aka saba gudanar da shi a garin Kano a duk shekara, wanda a bana zai kasance shi ne karo na 9 tun daga lokacin da aka fara shiryawa.

Babu shakka wannan taron ya kasance taro na farko da ake shiryawa a masana’antar finafinai ta Kannywood da ya shafe tsawon shekaru ana gudanar da shi ba tare da ya tsaya ba. 

Kuma wannan wani abin alfahari ne da Kamfanin Moɓie Image bisa jagorancin Malam Abdulkarim Muhammad ya samar ga ci gaban Kannywood Jihar Kano da ma Afrika gaba ɗaya 

A yanzu da yake lokaci ya fara tafiya a cikin wannan shekara ta 2026 ne ya sa muka nemi jin ta bakin Daraktan gudanarwa na taron KILAF AWARD 2026 Malam Muhammad Galadima domin jin irin shirin da suka yi na taron wannan shekarar. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Malam Muhammad Galadima kai ne Daraktan gudanarwa na taron KILAF AWARD da aka saba yi a duk shekara da yake mun shiga wannan shekara ko ya shirye shiryen ya kasance zuwa yanzu?

MALAM MUHAMMAD: To yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa, saboda ka ga zance da nake yi maka a yanzu ba a je ko’ina ba har mun samu finafinai guda 340 da suka shiga gasar wannan shekara kuma ƙasashen Afirka ne suka fi kowa yawan finafinai da suka shiga a wannan shekarar don mun lura cikin finafinan da aka shigar a yanzu Nijeriya da kuma ƙasar Masar su ne kan gaba wajen shigar da finafinai, kuma har yanzu ana matakin shigar da finafinai ne.

Amma za a ga kamar wannan taron na bana an fara shi da wuri musamman ta fuskar shigar da finafinai ko me ya kawo hakan?

E to abin da muka lura da shi akwai waɗanda suke son su shigar da finafinai a gasar, amma sakamakon babu lokaci sai ya zama wajen bayar da izinin shigowa ana samun tsawon lokaci, saboda haka sai muka ga dacewar mu fara da wuri yadda zuwa watan Afrilu an gama fitar da komai sai ya rage duk wanda zai zo daga wata ƙasa ya tanadi shirin zuwa don ya samu sauƙin samun biza. Don a shekarar da ta gabata muna ji muna gani akwai waɗanda za su zo daga ƙasar Zimbabwe da Yuganda amma ba su samu damar zuwa ba saboda ƙurewar lokacin. To wannan shi ne dalilin mu na fara shirin tun da wuri.

An sha shirya wannan taron tsawon shekaru, ko me ya bambanta wannan da sauran waɗanda suka gabata?

To bambanci mai girma shi ne a yanzu ita kanta KILAF AWARD ɗin tana ƙoƙarin ta ga ta zauna da ƙafarta, Wada ka ga tana ƙarƙashin Kamfanin Moɓie Image LTD , amma yanzu tana ƙoƙarin zama mai zaman kanta. Sannan kuma a cikin abubuwan da muka tsara mun shigar da sabbin shirye-shiryen da babu a baya. 

Daman dai kowa ya san akwai ajin koyar da finafinai na manya da masu koyo da muke yi, to a bana an faɗaɗa shi, ga tarurruka da jawabai da ake gudanarwa a BUK da sauransu. Kuma akwai abubuwa da dama waɗanda canje-canje ne domin a yanzu da yawa mun san ‘festiɓal’ da ake shiryawa a Arewa da ma Nijeriya wanda ganin yadda muke gudanar da tamu ya sa ake gayyatar mu, saboda tamu ta zama wani madubi yanzu kamar taron da ya gabata an nuna finafinai tun daga farkon taron har ƙarshe, duk da taron shi ne mafi ƙarancin lokaci da muka yi kwana uku, amma ai mutane sun ji daɗin yadda aka yi. Kuma shi kan sa taron bayar da kyautuka da aka yi mutane da yawa sun halarta.

To wanne irin buri aka ci wa shi taron na wannan shekara?

Gaskiya KILAF AWARD na wannan shekara muna da burin a samu halartar baƙi daga ƙasashen waje masu yawa don haka muna da shiri na musamman da muka yi na zuwan baƙin mu daga ƙasashen waje domin su ga yadda al’adun mu da kasuwanci da ci gaban da muke da shi 

Sai dai ana ganin ba ku cika bai wa ‘yan fim na Kannywood muhimmanci a taron ba.

To wannan ba haka ba ne, idan mutum daga wata ƙasa ta duniya mai nisa zai ɗauki taron KILAF AWARD nasa ne ya saka fim ɗin sa ya biya kuɗin jirgi ya zo ina kuma ga wanda yake a gida kuma a ke ganin shi ne ma ya kamata ya zama a gaba a wajen gayyata. To don haka idan mutum yana Kannywood a Kano a Zoo Road idan bai zo ba to mai za a yi masa. Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi don haka muna ganin kamar ba su shirya ba ne, kuma  za a yi musu uzuri da yawansu idan ƙarshen shekara ta zo suna aiki. Kuma na biyu da yake ita wannan Award ɗin ta finafinai masu gajeren zango ce su kuma a yanzu masana’antar ta fi yin finafinai masu dogon zango shi ya sa ba su cika shiga ba. To ni na yi musu wannan uzirin?

Amma ana ganin ita wannan gasar Turanci ya yi yawa a cikin ta, su kuma ‘yan Kannywood sun fi yin komai na su da Hausa kana ganin wannan ma bai taimaka wajen rashin shigar su ba?

To ai abin da yake faruwa duk ‘festiɓal’ ta duniya ana yin amfani da manyan yaren duniya ne. To abin da ya sa ka ga muna amfani da turanci saboda ya zama yaren da za a yi magana da kowa, amma kuma ba a taɓa samun wani ɗan Kannywood da ya zo KILAF AWARD ya ce zai yi magana da Hausa aka ce ba zai yi ba, don haka wannan ba dalili ba ne wannan ya sa babu wanda zan yi wa uziri, saboda na gayyaci wasu da baki na tura saƙo ta online, kullum a cikin gayyata nake, to ban ga abin da zan yi musu ba, in ba kowa so yake a bude ƙwaƙwalwarsa a saka masa ilimin ba.

Ko akwai wata buƙatar da kuke da ita a ɓangaren gwamnati?

To mu a cikin tsarin mu ba ma jam’iyya, kowa ya zo namu ne a matsayin mu na ‘yan ƙasa don haka magana ake ta ƙasa da kuma Jihar Kano, don haka duk abin da ya zo a kan ci gaban Jihar Kano, mu babu ruwan mu da waye yake kan kujera ko wacce jam’iyyar yake. Yanzu ka ga ai ba a taɓa samun wata gwamnati a Jihar Kano da ta bai wa KILAF AWARD lokaci kamar Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba. Ya yi ƙoƙari shekara biyun nan mun samu tallafi don haka muna godiya kawai dai abin da ba mu ji daɗi ba shi ne an yi taron gwamna bai halarta ba kuma bai tura wakili ba, sai kawai muka ji an yi taron ‘festiɓal’ a Legas ya halarta wanda mu kuma ga shi a garin sa muke yi, wannan shi ne ƙalubalen mu ga gwamnati.

To madalla mun gode.

Ni ma nagode sosai.

By ukarofi