Taron Tarihi da waƙoƙin Muhammadu Bawa Dan’anace: Ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Spread the love

Daga MUHAMMAD HABIB ALHASSAN 

Taron ƙasa da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto ta gudanar ya yi armashin samar da farin kai wa magwamatsa maɗauka kanwar ilimin tarihin rayuwa da waƙoƙin makaɗa Muhammadu Bawa Dan’anace ‘Yartsakkuwa Gandi Sakkwato. 

A zauren taro na Dr. Zayyanu Abdullahi a mazaunin dindindin na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Kwalkwalawa, Sokoto, taron da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar ta gudanar ya yi matuƙar armashin samar da farin kai wa dukkan waɗanda su ka gwamatsi malamai maɗauka kanwar ilimi da su ka yi bakacen Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Dan’anace ‘Yartsakkuwa Gandi Sakkwato a Waiwayen Shekaru Arba’in Masu Tarin Abubuwan Tunawa a Kansu. 

Wajen wannan muhimin taro da ya gudana daga ranar Jumu’a 3 zuwa Litinin 6 ga watan Afirilun shekarar nan miladiyya ta 2026, masu ruwa da tsakin lamunsa sun kuwa shanye raɗa bisa yin adalci wa taken taron, Dambe Wasan Maza – Kowa Ya Yi Hankali Ya Bar Ka: Tarihin Rayuwa da Gudummawar Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa Ga Harshen Hausa da Adabi da Al’adun Hausawa. Hasali ma dai, tattaunawar da aka yi, a jagorancin shugaban taro Maigirma Katukan Yauri Alhaji Abubakar Sadiƙ Yalwa, Manajan Daraktan Hukumar Raya Yankunan Samar da Wutar Lantarki ta Ruwa ta ƙasa (N-HYPPADEC), ta ƙayatar ainun.

Karin armshin taron ne, yadda a tsawon lokutan zaman tattaunawar, Babban Baƙo na Musamman Ministan ƙasan a Ma’aikatar Ayukka ta Tarayya Barista Bello Muhammdu Goronyo, yana wurin, tare da Mai Martaba Sarkin Mafara Alhaji (Dr.) Bello Muhammadu Barmo OON, da ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr.) Muhammadu Sa’ad Abubakar CFR, Mni. Shugaban Jami’ar ɗanfodiyo Farfesa Bashar Garba, MFR, (Tafidan Minanata) waɗari ne ya tsare yi domin tabbatar da cikakkar kulawar gaske wa mahalarta taron, a yayin da Daraktan Cibiyar Nazarin Hausa na Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo Farfesa Salisu Ahmed Yakasai ya yi halin girma da karimci wajen hidimar baƙi tun daga farko har ƙarshe.   

Masu magantawa kan jigon taron sun nuna cewa kowanensu ya fa zo wurin magana kan abinda aka yi tattaki da kundin bayani a hannu zuwa Sokoto a kai. Cike da himmar in-ba-ka-yi-bani-wuri, Baƙo Mai Jawabi Maigirma ɗanmadamin Birnin Magaji Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, da masu gabatar da jagaban maƙaloli uku, farawa da jakadan Jami’ar Bayero ta Kano a wajen taron, Farfesa Ibrahim Garba Satatiya (Talban Bunun Kano), da Farfesa Bashir Aliyu Sallau (Sarkin Askar Yariman Katsina kuma Hakimin Safana), da kuma Farfesa Suleman Adamu Sarɓi wanda Dokta Babangida daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ya wakilta, kowa ya baza sani. Daga maƙalar da kowanensu ya gabatar, an ɗaɗɗaki ruwan ilimin da ya tabbatar da cewa sauraren daka domin gane hanya shine aikin hankali ga wanda bai san gari ba.

Da ya ke shi abin buki da ɗai na buki ne, taron ya shaidi wakilci daga iyalan Makaɗa Muhammadu Bawa Dan’anace ‘Yartsakkuwa Gandi Sakkwato a jagorancin ɗansa Alhaji Yahaya Muhammadu Bawa ɗan’anace. Haka kuma, tun da komai rintsimi ba za a taɓa kwantar kai bambam da makitsiya ba, an samu wakilcin zuri’ar iyalan shahararren ɗan dambe Alhaji Abubakar ‘Yarkofoji wanda ake wa laƙabi Shagon Bakura Shagon Mafara. ɗansa Alhaji Sani Garba ’Yarkofoji shi ya jagoranci ayarin zuri’ar mahaifin nasa. Shi ma wani fitaccen ɗan dambe da ake kira Umaru Gundumi, da Malam Buhari wanda shi ɗa ne ga wani ɗan dambe mai suna Alhaji Muhammadu  Umaru Labbo da aka fi sani da suna Ango ɗangiye mutumen ‘Yartsakkuwa (shine wanda waƙarsa ita ce ta farko da Makaɗa Muhammadu Bawa Dan’anace ya fara rerawa a farkon fara shigarsa fagen waƙoƙin dambe), kazalika da masu abinda kansu, ayarin makaɗan dambe daga gidan Makaɗa Alhaji Muhammadu Bawa ɗan’anace a jagorancin Alhaji Yahaya Muhammadu Bawa Dan’anace, da kuma wani makaɗin dambe mai suna Sarki Muhammadu ɗanmoyi duk sun baje kolinsu, 

Mahalarta sun kwashi karatu, sun samu faɗakarwa da ilmantarwa da nishaɗantarwa da ta kaisu ga shagala domin, kan su ankara, har an kai ranar rufewa. A ƙarshen taro aka saurari jawabin godiya daga bakin Alhaji Yahaya ɗan’anace a madadin iyalan ɗan’anace, da kuma ƙarin wata godiya daga Alhaji Sani Garba a madadin iyalan gidan Shagon Bakura Shagon Mafara. Dukkansu, sun yi jinjina wa Sashen Nazarin Hausa da ita kanta Jami’ar Usman Danfodiyo ta Sokoto a kan mutuntawa da karramawar da aka yi wa iyayen nasu albarkacin sana’ar da suka rayu su ka yi fice a kanta har yanzu aka taru wajen bayyana ittifaƙin alfanun gudummawar musamman shi ɗan’anace ga raya harshen Hausa da al’adu da adabi. 

Malam Adamu Yunusa Ibrahim na Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo kuma Sakataren kwamitin shirya taron ya yi jawabin godiya a madadin Cibiyar, yana yaba matuƙar jindaɗin yadda mahalarta daga lungu da saƙo na faɗin Tarayyar Najeriya da wajenta har da ma tsallaken nahiyar Afirka zuwa ƙasashen nesa a kewayen duniya su ka ba da gagarumar gudummawa da muhimman bayanai ingantattu waɗanda daɓensu ya ji makuba sosai dangane da shi Alhaji Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa wanda aka raja’a da cewa ya sifantu a matsayin wani gunkin waƙar Hausa, haziƙin mawaƙin da baitocinsa ke ci gaba da zaburar da jaruntaka da ƙarfin hali a zukatan mayaƙa da masu sha’awar gadon adabin Hausa.

Daga cikin rubuce-rubuce da aka gabatar da waɗanda aka baje kolinsu a zauren taron akwai wani littafi mai suna “Mai Tsokana Yi Tsokanarka Mai Dariya Ka Ci Uwarka: Tarken Dabarun Tunzurawa a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa” wallafar Ibrahim Baba na Cibiyar Malamai ta ƙasa da ke Kaduna, da Saminu Sabo na Sashen Hausa na Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a da ke Nguru Jihar Yobe, da Bello Abdulƙadir Musana Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Kwalejin Ilimi ta Billiri Jihar Gombe. 

A wani sharhi a sakmakon wannan taro mai tarin albarka, da yawan jama’a sun yi nuni da cewa abin matuƙar a yaba ne gagarumar rawar da Baƙo Mai Jawabi Maigirma ɗanmadamin Birnin Magaji Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ya ke takawa a fagen jeranta alƙiblar tunanin ɗimbin masana wajen raya fannonan ilimin adabi.

Dokta Nasiru Wada Khalil, wani ma’abuci bibiyar tarurukan wanke ƙwaƙwalwa da na ƙara wa juna sani kan batutuwa majiɓinta adabi musamman al’adu da harsuna, yana jaddada cewa ba domin taimakawar ire-irensa ba, da ruwa ya ci tarihin adabin baka. Ya sifanta ɗanmadamin Birnin Magaji da malamin adabi da ya cancanci laƙabin “jami’ar adabi” bisa naƙaltar sirrin ƙwalelece bincike a kan kiɗa da waƙa ko tarihi daga Arewacin Najeriya zuwa Kudancin Jamhuriyar Nijar a cikin nazarin harshen Hausa da al’adun Hausawa.

Hasali ma, Dokta Khalil ya ƙara yin kira ga jami’o’in ƙasar nan su duba yiwuwar ba da digirin digirgir a bisa hujjar bayani sahihi kwatankwacin salon bincike da ƙungiyar UNESCO ta taɓa kira akai a wani taronta na 2003 domin taskace da wanzar da al’adu da hannu ba ya taɓawa, kamar kiɗa da waƙa da biki.

Za a iya tunawa, makomar ƙa’idojin Yarjejeniyar UNESCO ta 2003 kan kiyaye Al’adun Gargajiya Marasa Aiki tana nufin ta kare, ta kiyaye, kuma ta bunƙasa al’adun gargajiya waɗanda ba a iya taɓawa da hannu kamar harsuna, karin magana, waƙoƙi da raye-raye, bukukuwa, al’adun gargajiya da san’o’in gargajiya da ilimin gargajiya, da kuma al’adun rayuwa.

A taƙaice, babbar manufar yarjejeniyar UNESCO ce, kare al’adun gargajiya daga ɓacewa, da taimaka wa al’umma su ci gba da amfani da su, da tabbatar da cewa ana mutunta al’adun kowane yanki, kuma a ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe.

By ukarofi