
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Hukumar kula da harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, Alhaji Ibrahim Galadima ya rasu.
Tsohon Sakataren hukumar, Alhaji Sani Ahmed Toro ya sanar da haka a ranar Asabar.
Ahmed Toro, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne ya tabbatar wa Blueprint.ng faruwar al’amarin, idna marigayin ya rasu ne a safiyar ranar ne a Kano.
Ya kuma yi masa addu’ar fatan samun gafara da rahamar Allah.
An haifi Alhaji Ibrahim Galadima ne a ranar 14 ga watan Yunin 1951 a Fagge a Jihar Kano, inda ya riƙe muƙamin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa a Kano daga 1977 zuwa 1979.
Haka kuma shi ne shugaban majalisar wasanni ta jihar Kano tsakanin 1981 da 1983.
Bayan haka ne a 1984 aka naɗa shi a matsayin mamban kwamitin riƙo na Hukumar kula da Wasanni ta Ƙasa da dai sauran muƙamai a matakin jiha da ma ƙasa baki ɗaya.
A shekarar 1999 an naɗa Galadima Shugaban wakilan Nijeriya reshen Kano a gasar wasannin matasa na duniya da hukumar FIFA ta shirya.
Kazalika, an naɗa shi a matsayin shugaban hukumar NFA, wato NFF a yanzu a 2022.
