Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Alhaji Mohammadu Abdullahi, wanda aka fi sani da Baba Gombi kuma Sarkin Bakan Gombi, shugaban ƙungiyar mafarauta ta ƙasa (Professional Hunters Association of Nigeria), ya rasu yana da shekaru 100.
Marigayin, wanda ya shahara a matsayin jarumin mafarauci kuma jagora a harkar tsaron al’umma a yankunan karkara, ya rasu bayan ya bar tarihi mai cike da jarumtaka, sadaukarwa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
An haife shi a shekarar 1926 a ƙaramar hukumar Beneshak da ke Jihar Borno. Daga bisani ya koma Gombi a Jihar Adamawa a shekarar 1979, a lokacin tsohuwar Jihar Gongola, inda ya yi fice wajen haɗa kan mafarauta domin kare al’umma daga laifuka da hare-haren ‘yan tada ƙayar baya.
Baba Gombi ya kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan tsaron gargajiya a yankin Arewa maso Gabas, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da matsalolin tsaro ciki har da Boko Haram, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Ya rasu ya bar mata huɗu, ‘ya’ya 36, jikoki 56 da kuma jikokin jikoki 30.
Da yake jajanta rasuwar sa Shugaban ƙungiyar mafarauta ta ƙasa reshen Jihar Gombe, Rabi’u Baushe, ya bayyana rasuwar a matsayin babbar asara ga ƙasa baki ɗaya.
Ya ce, “Baba Gombi ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare al’umma musamman a yankin Arewa maso Gabas. Gudunmawar da ya bayar wajen yaƙi da matsalolin tsaro abin a yaba ne matuƙa.”
A shekarar 1987, marigayi Lamidon Adamawa, Alhaji Aliyu Mustapha, ya naɗa shi sarkin yaƙin Bindigan Arewa domin karrama jarumtaka da shugabancinsa.
A shekarar 2018 ne aka rantsar da shi a matsayin Shugaban ƙungiyar mafarauta ta ƙasa, inda ya ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin mafarauta da hukumomin tsaro na gwamnati, musamman wajen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.

A lokacin tsananin rikicin Boko Haram a shekarar 2015, mafarauta ƙarƙashin jagorancinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen kwato garin Gombi da wasu yankuna da ke kewaye, inda suka taimaka wajen dawo da zaman lafiya.
Haka kuma, sun taimaka wajen kuɓutar da ɗaruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su a sassan Jihar Adamawa ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
An san Baba Gombi da tawali’u, kishin ƙasa da jajircewa, kuma ya samu yabo daga gwamnatoci da hukumomin tsaro saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen yaƙi da tada ƙayar baya da sauran miyagun laifuka.
Al’umma na ci gaba da tuna shi a matsayin gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa domin tsaron jama’a, wanda tarihinsa zai ci gaba da zama abin koyi a Najeriya.
