Gwamnan Bauchi ya soke shirin koma wa APC kan rashin cimma yarjejeniyar 60-40

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi ta kawo ƙarshen tattaunawa da jam’iyya mai mulki (APC) a hukumance bayan da ɓangarorin biyu suka gaza cimma yarjejeniya akan sharuɗɗan da ake buƙata na sauya salon siyasar gwamnatin jihar.

Shugaban PDP a jihar, Sama’ila Burga ya bayyana haka a yau Asabar yayin hira da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke cikin garin Bauchi.

Ya bayyana cewa, bayan tattaunawa tsakanin Gwamna Bala Mohammed da wasu jami’an jam’iyyar, da kuma a matakin ƙasa da ya haɗa Mataimakin Shugaban ƙasa, Kakakin Majalisar Wakilai da wasu tsofaffin gwamnoni guda uku, APC ba ta cika sharuɗɗan da PDP ta gindaya ba na yiwuwar haɗa hannu.

Burga ya ce, yunƙurin fara tattaunawa akan al’amarin ba daga PDP ba ne, saidai APC ita ce ta nemi jam’iyyar da batun, wanda aka gaza cimma matsaya a kai.

Da yake warware batun cewa ana shirin cimma matsaya akan buƙatar raba muƙaman gwamnati akan kaso 60 da 40, Burga ya tabbatar da cewa APC ta ki amince wa hakan bisa wasu dalilai da ta dogara da su.

A cewarsa, irin buƙatar ba sabon al’amari ba ne ga Bauchi domin an yi makamancin haka a wasu sassan ƙasar inda aka raba muƙaman gwamnati a tsarin matakan 70 da 30 yayin sauya sheƙa.

Ganin cewa APC ta ƙi amincewa da tsarin ya sa aka gaza cimma yarjejeniya yayin zaman don haka gwamnan da ‘yan PDP da sauran masu ruwa da tsaki a jihar suka koma nazari akan zaɓin da suke da su a siyasance.

By Babaji