Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni na nuni da cewa sansanin siyasar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara nuna goyon baya ga Mataimakin Gwamnan Jihar Legas, Kadri Obafemi Hamzat, a matsayin wanda ake shirin tsayarwa domin maye gurbin gwamnan jihar a babban zaɓen 2027.
Wannan ya biyo bayan bayyana goyon baya a fili da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ikeja, James Faleke, ya yi ga Hamzat, lamarin da masana siyasa ke fassarawa a matsayin wata alama daga cikin gida na masu tsara shugabanci a jihar Legas.
Rahoton ya nuna cewa furucin Faleke ba wai ra’ayi na kansa ba ne kawai, illa wata hanya ce ta isar da saƙo daga manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, musamman ma ɓangaren da ke ƙarƙashin jagorancin Tinubu.
Masu lura da al’amuran siyasa sun ce Faleke, wanda ya dase yana cikin tsarin siyasar Tinubu, ba ya yawan yin irin waɗannan kalamai masu nauyi sai da amincewar manyan shugabanni.
Saboda haka, ana kallon wannan mataki a matsayin wata alama cewa an riga an tsayar da Hamzat a matsayin wanda aka fi so ya gaji gwamna Babajide Sanwo-Olu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Faleke ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su marawa Hamzat baya gabanin zaɓen fidda gwani, yana mai cewa ya kamata a mara masa baya domin ya zama gwamnan Legas daga shekarar 2027 zuwa 2035.
Bayan wannan goyon baya a fili, akwai alamun cewa Majalisar Shawarwari ta Gwamnati (GAC), wadda ita ce babbar cibiyar yanke hukunci a APC ta Legas, na karkata zuwa ga wannan matsaya. A al’ada, ra’ayoyin GAC na nuna akalar tunanin manyan masu faɗa a ji a cikin sansanin Tinubu.
Idan wannan haɗin kai ya tabbata, Hamzat zai samu cikakken goyon baya daga manyan jiga-jigan siyasa, ciki har da tsohon gwamna Babatunde Fashola da kuma gwamna mai ci yanzu Sanwo-Olu, waɗanda ake kallon su a matsayin amintattun mambobin wannan sansani.
Tarihi ya nuna cewa Hamzat ya taɓa aiki a matsayin mai ba da shawara ga Fashola a lokacin da yake minista tsakanin 2015 zuwa 2019, kafin daga bisani ya zama mataimakin gwamna. Haka kuma, shi ne kaɗai mataimakin gwamna da ya yi wa’adi biyu tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Sai dai kuma duk da wannan daidaituwar fahimta, ana sa ran za a iya fuskantar ƙalubale, domin tsohon gwamna Akinwunmi Ambode na da burin komawa fagen siyasa, wanda hakan zai iya kawo cikas ga wannan tsari da ake ƙoƙarin daidaitawa.
A halin yanzu, yayin da ake tunkarar zaɓen fidda gwani na APC, furucin Faleke ya sauya tattaunawar daga hasashe zuwa wani tsari mai bayyana, inda ake kallon Hamzat ba kawai a matsayin ɗan takara ba, har ma a matsayin wanda aka amince da shi daga sansanin Tinubu domin jagorantar jihar Legas a gaba.
