(Ci gaba daga makon jiya)
Daga MUKHTAR YAKUBU
A daidai lokacin da aka samu sauyin shugabanci a tashar talabijin ta ALGAITA TV wadda take haska finafinan Hausa na masana’antar Kannywood bayan saukar shugaban ta na farko Umar Sani Kofar Mazugal inda aka maye gurbin sa da sabon shugaba Mu’azzam Idi Yari. A yanzu haka an samu wasu canje-canje da kuma ci gaban tashar domin tafiyar da ita daidai da bukatar al’umma. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da sabon shugaban Mu’azzam Idi Yari domin bayyanawa masu karatu inda alkiblar ALGAITA TV ta sa a gaba, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:
MANHAJA:To ya za ka kwatanta irin nasarorin da tashar ta samar a yanzu?
MU’AZZAM: Ai daga fitowar ALGAITA TV mutane da yawa sun iya fita su je su yi furodusin, saboda sun gamsu ba sai da wane da wane ba ne za su iya furodusin saboda da ƙarfin da suke da shi na kaiwa manyan gidajen talabijin da sai an fiya kuɗaɗe masu yawa, don haka sai ci gaba ya zo wanda yanzu za ka ga kullum aiki ake fita wanda a ɗan lokaci masana’antar ta ƙara faɗaɗa, don ko daga lokacin da na karɓi wannan shugabancin kullum mutane suna kira na domin su kawo fina-finai a saka musu a tashar talabijin ta ALGAITA TV to ko a iya nan an samu ci gaba. Kuma ka tuna muna da manyan fina-finai da muke haskawa kamar irin su ‘Garwashi’ Gidan Sarauta’ ‘Matan Gida’ da sauran manyan fina-finai da za su zo nan gaba.
Mun san duk wani abu da yake tare da nasara akwai ƙalubale. Ko wanne ƙalubale kuke fuskanta?
To akwai ƙalubale amma mu mun ɗauke shi a matsayin darasi, kamar a yanzu za ka ga kowa ya zo yana son a ba shi lokaci wanda wani lokacin abin ya kan zo mana da matsala, amma dai hakan mukan ɗauki abin a matsayin nasara saboda karɓuwa da muka samu ne, saboda muna cikin tashar talabijin da ake kallo masu nuna fina-finai na al’adar Hausawa saboda gidan talabijin din na ‘yan Kannywood ne babu wani abu da zai zo da shi wanda bai shafi ‘yan Kannywood ba, don haka za ka ga matasan mu sun samu aiki don haka gidan talabijin din ya zo da nasara da kuma albarka mai yawa ita masana’antar Kannywood, musamman ga masu tasowa nan gaba.
A yanzu da yake kai sabon shugaba ne , akwai wasu sabbin tsare-tsare da ka zo da shi ko dai za ka ɗora ne daga inda ka samu?
To shugabancin da aka samu sauyi na gudanarwa ne, kuma tashar ce ta bunkasa take da bukatar hakan, saboda yadda masu huddar da muke da su kullum karuwa suke yi, don haka akwai bukatar a fadada a karo mutane da za su biya bukatar mutanen da a kullum suke karuwa domin a samu sauƙi, kuma ba alfahari nake ba watakila an ga dacewa ta ne a bangaren shi ya sa aka dora ni saboda ina da kyakkyawar alaka da kowane Furodusa kuma ina da burin na ga masana’antar ta ci gaba, kuma wannan shi ne abin da tashar talabijin ta ALGAITA TV take buƙata a samu mutumin da zai iya mu’amala da kowa domin ‘yan Kannywood su samu hanyoyin da za su yi kasuwancin su cikin natsuwa.
Shi wannan gidan talabijin ɗin na Algaita TV ba shi kadai ba ne a yanzu na ‘yan Kannywood akwai wasu. Ko ya kuke gogayya da su wajen gudanar da aiki?
To daman abin da ya kamata kenan a ce an samu gidajen talabijin kamar guda goma, kuma a yanzu an fara samu wanda a yanzu kowa jajircewarsa ce za ta sa ya yi nasara, kuma muna farin ciki da samu karin wasu, saboda masana’antar Kannywood babba ce, yanzu gidan talabijin na Algaita TV ana kallon sa a ƙasashen Kamaru Ghana Nijar da sauran ƙasashen da duk Bahaushe yake. Shi ya sa za ka ga muna zuwa da abubuwan da suka shafi al’adu na Hausawa da suke wasu ƙasashen, kuma a yanzu cikin shirin da muke da shi, za a samar da gidan talabijin din na Algaita TV Online da za a rinka bibiyar shafin a waya wanda wannan nasara ce sosai kuma ina sha Allahu nan da shekara guda za a ga abin da ya fi haka.
Don haka ina godiya ga duk waɗannan mutane masu kishin da suka samar da gidan talabijin din, gaskiya ba ni da bakin da zan gode musu, saboda ni ina kishin masana’antar, don haka idan wasu mutane sun zo sun ce bari mu taimaki masana’antar, to za mu yi maraba da su kuma za mu ba su haɗin kai na ganin an sanar da ci gaban masana’antar.
Kuma muna maraba da duk wanda ya zo gidan talabijin din domin mu ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da shi, don haka kowa ya zo gidan talabijin din na Algaita TV na kowa da kowa ne, duk wani furodusa da yake da kishin masana’antar ya zo Algaita TV muna maraba da kai. Ina fatan Allah da ya ɗora ni a kan wannan shugabancin da ya dafa mini domin na kai ga nasarar da muke buƙata.
To madalla mun gode.
Ni ma na gode Sosai.
