MACBAN ta yi Allah-wadai da kisan gilla a Filato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

ƙungiyar Makiyaya ta Nijeriya, wato Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 30 a birnin Jos na Jihar Filato, tare da gargaɗin masu amfani da kalamai masu tunzura jama’a.

Shugaban ƙungiyar, Baba Othman-Ngelzarma, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan lamari mai muni wani sabon tunatarwa ne na yadda zubar da jini ke ci gaba da addabar jihar.

Ya bayyana cewa irin wannan tashin hankali bai kamata a bar shi ya ci gaba ba, yana mai jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma duk waɗanda abin ya shafa.

A cewarsa, yawaitar rikice-rikice a Filato na ci gaba da lalata zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’umma, lamarin da ke barazana ga dunƙulewar ƙasa baki ɗaya.

Shugaban ya nuna damuwa kan yadda jihar ta daɗe tana fama da rabuwar kai, rashin amincewa da juna da kuma hare-haren ramuwar gayya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan mummunan yanayi.

Haka kuma, ya zargi wasu daga cikin shugabannin addini da masu faɗa a ji da taka rawa wajen rura wutar rikici ta hanyar kalamai marasa kima da ke haddasa rarrabuwar kawuna, maimakon su ƙarfafa zaman lafiya da juriya.

Ya jaddada cewa wajibi ne shugabannin addini su zama ginshiƙin haɗin kai da zaman lafiya, ba wajen tunzura jama’a ba.

Don haka, ya buƙaci dukkan shugabannin addini, na gargajiya da na al’umma da su yi taka-tsantsan, su ƙarfafa tattaunawa, tare da ƙoƙarin rage zafin rikice-rikice a tsakanin al’umma.

Ya kuma tunatar da cewa kalamai na da matuƙar tasiri, musamman a irin yanayi mai sarƙaƙiya, inda za su iya ko dai kawo waraka ko kuma ƙara ta’azzara matsala.

Dangane da ɓangaren tsaro, MACBAN ta buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakai masu tsauri da kwarewa, tare da gano waɗanda ke da hannu wajen tayar da rikici ko ta hanyar aikatawa kai tsaye ko kuma ta hanyar kalamai.

ƙungiyar ta ce wajibi ne a binciki duk masu laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu, ba tare da nuna son kai ba, domin rashin hukunta masu laifi na ƙara ƙarfafa aikata laifuka.

Haka kuma, ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri domin gano masu hannu da shuni da ke ɗaukar nauyin rikice-rikicen, tare da ƙara tsaurara tsaro a yankunan da ke cikin haɗari.

A ƙarshe, Baba Othman-Ngelzarma ya jaddada cewa mutuncin rayuwar ɗan Adam abu ne da ba za a yi sulhu a kansa ba, yana mai cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗa kai da gwamnati, ƙungiyoyin farar hula da shugabannin al’umma domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a Filato da ma faɗin Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaskiya domin kawo ƙarshen zubar da jini.

By ukarofi