Daga AISHA ASAS
*Masu amfani da Facebook sama da miliyan 533 ‘yan Italiya na iya shiga ƙarar neman diyya
*Meta ta ce hukuncin bai nuna ta taka doka ba, ta kuma yi hasashen za a watsar da ƙarar
Wata kotu a birnin Milan na ƙasar Italiya ta amince da ci gaba da wata ƙarar gamayya (class action) da wata ƙungiyar kare haƙƙin masu amfani da kafafe ta shigar kan kamfanin Meta Platforms, dangane da zargin satar bayanan sirri da ta shafi masu amfani da Facebook.
A cewar umurnin kotun da aka bayar a ranar Talata, wannan matsala ta satar bayanai ta faru ne tsakanin watan Janairu na 2018 zuwa Satumba na 2019, kuma kamfanin Meta ne ya bayyana ta a shekarar 2021. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya shafi kimanin masu amfani da Facebook miliyan 533 a faɗin duniya baki ɗaya.
ƙungiyar masu kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki ta CTCU ce ke jagorantar wannan ƙarar, inda take neman a biya diyya ga masu amfani da shafukan sada zumunta waɗanda suka rasa, ko suka ji tsoron rasa iko da bayanansu na sirri, abin da ake zargin ya saɓa wa dokar kare bayanai ta Tarayyar Turai wato GDPR (General Data Protection Regulation).
Wani majiya a shari’ar ya bayyana cewa, akwai yiwuwar kusan masu amfani da Facebook miliyan 35 a ƙasar Italiya kaɗai sun shafa daga wannan satar bayanai, lamarin da ke nuna girman illar da ake magana a kai.
Sai dai a martanin da ta mayar, Meta ta nuna rashin amincewa da hukuncin kotun, tana mai cewa wannan hukunci na matakin farko ne kawai na shari’a, kuma bai tabbatar da cewa kamfanin ya karya kowace doka ba.
Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce: “Muna girmama kotun, amma ba mu yarda da wannan hukunci ba. Wannan dai hukunci ne na tsari kawai, kuma bai tabbatar da cewa Meta ta karya wata doka ba. Muna da ƙwarin gwiwa cewa wannan ƙarar ba ta da tushe, kuma daga ƙarshe za a yi watsi da ita.”
Lamarin na ƙara jefa haske kan yadda manyan kamfanonin fasaha ke fuskantar matsin lamba daga hukumomi da ƙungiyoyi masu kare haƙƙin masu amfani, musamman kan batun tsaron bayanai da sirrin jama’a.
